Ilimi

Tasiri Da Amfanin Schools Of Nursing Gare Mu A Yanzu (007)

Spread the love

•Shin da gaske ne samun Admission a School of Nursing, yana wahala ?

•Shin da gaske ne School of Nursing tana da tsada ?

•Shin da gaske ne ana bada alawus a School of Nursing ?

♦A wannan program ɗin kashi na bakwai (7) bayan nazari da za mu yi akan tambayoyin da ke sama, za kuma mu yi bayanin tsarin Neman Admission a School of Nursing, da rabe-raben su;

Schools of Nursing, ko Colleges of Nursing and Midwifery, dama dukkan sauran makarantun karatun lafiya da mu ke da su a matakin Diploma, kan zamo wa makarantu masu farin jini, inda hakan yasa ɗalibai ke tururuwar neman admissions a irin makarantun, kuma galibi schools of nursing suna da adadin mutanen da aka basu umarnin ɗauka a kowace shekara (aka sahale musu), misali: idan ana buƙatar ɗalibai 100, akan iya samun ɗalibai sama da 300 suna neman admission, wanda hakan ke sanyawa dole ɗalibai kusan 200 ba za su samu admissions ba. Bugu da ƙari makarantun basu da yawa a kowace jiha, hakan yasa ake musu yawa.

√• Abin tambayar, shin admission ɗin yana wahala kenan ?

Abin yana danganta ne da jihar da ɗalibi yake, hakan kuma na nufin cewar, a wasu jihohin Admission ɗin yana wahala, yayin da a wasu kuma baya wahalar samu sosai. Babban ƙalubalen dai shi ne haye jarrabawar Wedding, da galibin Schools of Nursing suke shiryawa!.

√• Yaya batun biyan kuɗin registration a Schools of Nursing ?

Tabbas akwai dalilai da yawa, da ke nuna yadda kuɗin rijistar ɗalibai yake da tsada a Schools Of Nursing, duk kuwa da cewar ba haka abin ya ke ba, galibi ɗalibai saboda yadda su ke son karatun su kan je wasu jihohin su yi, wanda hakan yasa su ke ganin tsadar kuɗin makarantar, domin kuwa su ba ƴan jihar bane, kuma a tsarin kowacce makarantar gaba da Sakandire mallakin jiha, ɗaliban da ba ƴan asalin jihar ba, suna biyan kuɗin registration fiye da adadin da ƴan jihar su ke biya, wannan yasa wasu suke ganin tsadar kuɗin makarantar, ko da yake duk da haka tsadar kuɗin makarantar yana danganta ne daga makaranta zuwa makaranta, a wasu lokutan kuma ɗalibai kan haɗe Schools of Nursing na gwamnati, da masu zaman kansu, sai su dinga ganin kamar dukka Schools of Nursing ne ke da tsadar. Anan kuwa jan hankalin mu shi ne karatun Nursing, karatu ne wanda ya ke da matuƙar muhimmanci, kuma nan da nan ɗalibai su ke samun aiki da zarar sun kammala, dan haka ko da yana da tsada, in dai da hali, to Iyaye su daure su biya wa ƴaƴayen su.

√• Shin ko ana biyan alawus duk wata, ga ɗaliban da ke karatun Nursing ?

Wannan amsar Eh ce, kuma A’a, domin kuwa makarantun Nursing sun banbanta, akwai waɗanda su ke ƙarƙashin Polytechnics, wanda su ke ND da HND Nursing, Sannan akwai waɗanda su ke ƙarƙashin ma’aikatar lafiya ta jiha (mallakin jihohi), har ila yau akwai kuma waɗanda su ke ƙarƙashin Teaching Hospitals, galibi su kuma na gwamnatin tarayya ne, don haka ba kowacce jiha ce take biyan ɗalibai alawus ba, kamar yadda kuma ba kowacce makarantar Nursing ce idan ɗalibi ya na karatun za ta dinga ba shi alawus ba, amma galibin jihohin suna biyan alawus ɗin ne ga makarantun da ke ƙarƙashin su, koma yaya ne, mu fatanmu samun ilimin, ba batun alawus ba.

Batun tsarin neman admission da samun sa, a makarantun Schools of Nursing, wannan ita ce manufar da ta sanya mu ka buɗe group na musamman ga ɗalibai ma su son zuwa School of Nursing, ko kuma makarantun Health Technology, ko Schools of Hygiene, da sauran su, domin yi wa ɗaliban cikakken bayani tare da kuma ji daga bakin wasu da suka riga suka kasance ɗaliban Nursing ɗin, dan haka waɗanda suke cikin group ɗin daga ɗaliban Nursing, sai masu nema.

Makarantun sun kasu kashi-kashi, kamar yadda na faɗa, dan haka kuwa tsarin nema da samun admissions ɗin su shi ma ya banbanta, duk da cewar akwai abubuwa kusan iri ɗaya, da su ke tsakanin wasun su.

Bari mu jero wasu kaɗan daga cikin rabe-raben makarantun, domin mu fayyace muku komai dalla-dalla, akan yadda ake samun admission, ko nema:

• Schools Of Nursing (Under State Ministry of Health).

• Schools Of Health Technology (Under State Ministry of Health).

• Schools Of Nursing (Under Teaching Hospitals).

• School Of Post Basic Nursing (National Orthopaedic Hospital Dala, Kano).

Schools Of Hygiene (Under State).

Polytechnics (waɗanda suke Nursing).

Galibin makarantun da ke ƙarƙashin Ministries of Health na jihohi, ana sayar da Forms ɗin su ne ƙarkashin Ministry of Health, a wasu jihohin, yayin da a wasu kuwa a ƙarƙashin makarantar ake sayarwa, haka zalika, bayan cika form ɗin, galibin su ba a buƙatar JAMB UTME, sai dai ana shirya wa ɗalibai jarrabawa, wacce za ta tantance waɗanda za a ɗauka, da ma waɗanda baza a ɗauka ba, kuma anan ne galibi ake zubar da mafi yawan ɗalibai, sakamakon rashin cin jarrabawar, ya yin da wasu daga cikin su kuwa suke buƙatar JAMB, idan ya kasance karatun Nursing ɗin da su ke yi ND ne.

Polytechnics, waɗanda su ke Nursing (ND/HND) : wannan ɓangaren kuma dole ana buƙata ɗalibai su yi JAMB, kuma dole ne su samu adadin makin da ake da buƙata, kafin samun Admissions. Kuma galibin Polytechnic ɗin da su ke Nursing, ɗalibai sun fi samun su idan su ka nema, matuƙar sun ci JAMB UTME, kuma su na da 5 Credits a darussan Mathematics, English Language, Chemistry, Physics, da Biology (za mu lissafo Polytechnics ɗin da su ke Nursing ND, a program na gaba).

Makarantun Nursing ɗin da su ke ƙarƙashin Teaching Hospitals : Su ma galibin su ba sa buƙatar JAMB, sai dai suna buƙatar ɗalibai su cika Form, kuma suna shirya Interview, ko jarrabawar tantancewa, inda su ma galibi a nan su ke zubar da ɗalibai, amma matuƙar ɗalibi ya ci, to za a ba shi Admission, dan haka dole sai an dage.

A taƙaice dai, abu na farko: dole ne ɗalibai su cika dukkanin sharuɗɗan neman Admission (admission requirements), na makarantar da su ke nema, baya ga haka kuma, dole su ci jarrabawar da aka shirya, kuma hakan yana nufin dole ne ɗalibai su dage.

Manufar mu dai, ita ce ɗalibai su tsaya da ƙafafun su, ta hanyar inganta ilimin su a kowanne ɓangare.

ASOF ta ku ce, kuma ta kowa ce!.

MASU ƊAUKAR NAUYI : ƘUNGIYAR AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM, DA TALLAFIN : JARIDAR MIKIYA.

     08086251045.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button