Ilimi

Tasiri Da Amfanin Schools Of Nursing Gare Mu, A Yanzu (008)

Spread the love

Banbancin da ke tsakanin Nursing, da Midwifery :

Ɗaliban da ke shirin shigowa ɓangaren lafiya, musamman Nursing, na yin nazarin shin wanne ɓangare ya kamata su shigo, musamman ma Mata, ko da ya ke daman ɓangaren Midwifery mata ne kaɗai ke shigar sa, domin kuwa ya shafi ɓangaren su ne, wato haihuwa, da rainon ciki.

A yau, za mu kawo kaɗan daga cikin banbance-banbancen da ke tsakanin Midwifery, da Nursing. Ga su kamar haka :

• Nursing, ya ƙunshi ɓangaren aikin jinya ne daban-daban, da kuma taimaka wa marasa lafiya, da ma likita, wajen gudanar da aikin kula da marasa lafiya. Yayin da Midwifery kuwa ya ƙunshi ɓangaren ɗaukar ciki, rainon sa, da ma haihuwa, kuma su ne su ke taimakon mata a lokacin ɗaukar ciki, naƙuda, da bayan haihuwa.

• Nurse, na iya aiki a wurare daban-daban na aikin jiyya, yayin da Midwifery kuwa sun fi yin aiki ne a ɓangaren naƙuda da haihuwa.

• Nursing, ya ƙunshi wani ɓangare na rukunin kwasa-kwasan Midwifery, sai dai bai kai a ce za su iya aiki a matsayin ungozoma ba, kamar yadda Midwifery su ma su ke da ɓangaren aikin jinya, wanda bai kai su yi aikin jinya kamar Nursing ba.

• Ɗaliban nursing za su iya ƙwarewa a fannonin:

<> Ophthalmic Nursing.

<> Orthopedic Nursing.

<> Psychiatric Nursing.

<> Anaesthetic Nursing.

<> Otorhnolaryngology (ENT) Nursing.

<> Peri-Op Nursing.

Da sauran su.

Yayin da Midwifery kuwa, ba za su iya ba, sai sun samu horo a nursing (misali : Post Basic Nursing), kafin su samu lasisi, a matsayin Nurses ma su rijista.

• A ɓangaren Nursing, ɗalibai maza da mata ne, ya yin da ɓangaren Midwifery kuwa mata ne zalla.

• Nurse ɗin da ke son zama Midwifery, dole ne ta yi rijista a Post Basic Midwifery, na tsawon watanni 18, sannan ta ci jarrabawar da hukumar Nursing and Midwifery Council of Nigeria (NMCN) ta ke shiryawa, haka ma ɗalibar Midwifery da ke son zama Nurse, za ta yi program na tsawon watanni 18, a Post Basic Nursing, tare da cin jarrabawar da hukumar kula da ma’aikatan jiyya da ungozoma ta Najeriya (NMCN), ta ke gudanarwa.

Dukkannin su (Nursing da Midwifery), programs ne na shekaru 3, kuma waɗanda su ka kammala kowanne ɗaya daga cikin ɓangarorin, su na iya samun shiga kai tsaye zuwa Jami’a, don yin karatun Bachelor of Nursing Science, a Degree.

MASU ƊAUKAR NAUYI : ƘUNGIYAR AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM, DA TALLAFIN JARIDAR MIKIYA.

      08086251045.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button