Ilimi

Tasiri Da Amfanin Schools Of Nursing, Gare Mu, A Yanzu (009)

Spread the love

• Community Nursing :

A dukkannin programs ɗin da mu ka yi akan nursing, daga na ɗaya zuwa na takwas, mun yi ta bayanin cewar; Nursing yana da ɓangarori daban-daban, dan haka, a yau kacokan, za mu yi magana ne akan, Community Nursing.

Community Nursing, program ne na shekaru 2, (semester huɗu), kuma hukumar ”Nursing and Nursing Council of Nigeria (NMCN)” ta amince da shi, haka zalika, ita ta ke bada lasisin sa, dan haka wanda ya yi Community Nursing, ba zai zama RN nursing ba, sai dai, za su zama Licensed Community Nurses (LCN) ne. Kuma an tsara community nursing ne, da nufin horas da ɗalibai kan ƙwarewar aikin jiyyar na al’umma, tare da ba su Ilimi, da kuma ƙwarewar ayyukan asibiti, kuma su na buƙatar wannan Ilimi ne, dan zama ma’aikatan jiyya na al’umma, masu lasisi (LCN), dan ba da kulawar jinya ga ɗai-ɗaikun mutane, ko marasa lafiya, da kuma taimaka musu, a ayyukan da za su inganta kiwon lafiya.

Kuma su na ba da taimakon gaggawa, kulawa, da ma shawarwari, ga marasa lafiya.

Kulawar ta haɗar da; ɗaukar samfurin marasa lafiya, bayar da magunguna, sanya ido kan marasa lafiya, ɗaukar bayanai, da kuma bayar da Ilimin kiwon lafiya, ga al’umma.

Community Nursing, ana yin sa a wasu daga cikin makarantun Nursing, ko kuma ƙarƙashin Teaching Hospitals, kamar makarantar Kasimu Kofar Bai, School of Nursing, Katsina, ita ma tana yi.

An kuma, ƙirƙiri program ɗin ne, domin jagoranci, da aiwatar da ayyukan jiyya, da kiwon lafiya, ga al’umma, a matakin farko, a matsayin su na masu ba da agajin gaggawa, ta hanyar kula da marasa lafiya. Ɗaliban Community Nursing, galibi su na aiki ne, a Primary Health Care.

Maza da mata, dukka su na da damar yin Community Nursing.

Community Nurses, masu lasisi, za su iya aiki a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (Primary Health Care).

Community Nurses ɗin da ke son ci gaba da karatun su, domin zama Registered Nurses (RN), za su yi Program na shekaru biyu ne, a School of Nursing, kafin su samu damar zama RN.

• Abubuwan da ake buƙata, domin neman Admission, a Community Nursing:

√• 4 Credits, wanda ya haɗa da, darussan : English, Biology, Chemistry, da Physics, a guda daga cikin jarrabawoyin WAEC, NECO, ko NABTEB.

√• Za a buƙaci ɗalibai, su rubuta jarrabawar shiga, da makarantar,za ta gudanar.

√• Za a gayyaci waɗanda su ka yi nasara a jarrabawar, zuwa Interview.

√• Za a bada Admission, ga waɗanda su ka yi nasara a interview.

√• Ɗaliban za su samu horo
na watanni shida, bayan nan kuma, makarantar
za ta sake gudanar da jarabawar gabatarwar zangon farko.

√• Ɗaliban da su ka yi nasara a jarrabawar ne kuma, hukumar Nursing and Nursing Council of Nigeria, za ta tantance, domin zama cikakkun ɗalibai, yayin da kuma ɗaliban da ba su yi nasara ba, za a cire sunayen su.

Harkar karatun nurse, ta kowanne ɓangare, maganar gaskiya bata son wasa, saboda harkar lafiyar ɗan adam ce, dan haka dole ne a dage.

Allah ya bamu nasara.

MASU ƊAUKAR NAUYI : ƘUNGIYAR AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM, DA TALLAFIN JARIDAR MIKIYA.

       08086251045.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button