Ilimi

Wata Ƙungiyar Ceto Ɗaliban Mai Zaman Kanta (NGO) Mai Suna (Taraba State Students Rescue Club) Ta Gudanar Da Wani Taron Wayar Da Kai Na Kwana Guda Kan “Muhimancin Illimin ‘Ƴa’ya Mata, Da Illar Shan Miyagun Ƙwayoyi.

Spread the love

Ɗaliban Kwalejin Illimi Ta Peacock Da Ke Jalingo A Jihar Taraba Sun Karɓi Baƙuncin Wata Ƙungiyar Ceto Ɗaliban Mai Zaman Kanta (NGO) Mai Suna (Taraba State Students Rescue Club) Inda Ta Gudanar Da Wani Taron Wayar Da Kai Na Kwana Guda Kan “Muhimancin Illimin ‘Ƴa’ya Mata, Da Illar Shan Miyagun Ƙwayoyi.”

Da ya ke jawabi kan maƙasudin samar da shirin, Shugaban ƙungiyar, Comrade Abdulrazak Abubakar Dabo, wanda ya samu wakilcin Babban Sakatarenta, Usama Habibi Issa, ya ce an samar da shirin ne domin bayyana buƙatar da ke akwai ta haɓɓaka rayuwar al’umma, ta hanyar samar da ingantaccen Ilimi, ga yara, musammanma mata.

Inda yace: ”Akwai buƙatar mu yi duba a kansa, duba da irin muhimmancin da ke tattare da shi, domin Ilimantar da mace guda, tamkar Ilimantar da duniya ne baki ɗaya”.

Da ta ke gabatar da muƙala mai taken, ”Ilimi da muhimmancinsa ga cigaban muhalli”, Mawallafiyar Jaridar Ziti, kuma Shugabar Mata, a kafafen yaɗa labarun jihar Taraba, ta nusar kan alfanu daban-daban da ke tattare da Ilimin yara mata ga zamantakewa, inda ta buƙaci Iyaye da su tabbatar sun sanya dukkannin yaran su a makaranta, musamman ma yara mata.

Tana mai cewa, ”Ilimantar da yara mata ya na da muhimmanci wajen ciyar da al’umma gaba, dan haka muna buƙatar mata da za su shiga a dama da su, a harkokin siyasar jihar Taraba, kuma mu sani muddin bamu samu Ilimi ba, babu yadda za mu shiga a dama damu, ba zai yiwu ba, hakane ?, to wannan guda ne daga cikin muhimmancin samar wa da yaranku Ilimi, ga cigaban muhalli.”

Mu dawo jihar mu ta Taraba, idan mu ka kaɗa ƙuri’unmu ga ɗan takara na gari, a ƴan watannin da ke tafe, za mu samu gwamnatin da za ta magance mana matsalolin da ke addabarmu a zamantakewa, kamar shaye-shaye, da ma samarwa yara mata Ilimi.

”Ina shawartarku da ku tabbatar kun karɓi katinan zaɓukan ku na din-din-din, ku kuma zaɓi ƴan takarar da su ka damu da jama’a, domin samun sauƙi kan halin da mu ke ciki”.

A nasa jawabin, wakilin hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, reshen jihar Taraba, cewa ya yi wajibi ne matasa su gujewa ɗabi’ar shaye-shaye, duba da ire-iren illolin da ta ke da su, ga al’umma baki ɗaya.

Inda ya ce, ”Babu yadda kuma za mu iya kawo ƙarshen wannan matsala, har sai mun dakatar da abin daga kan mu, domin wajibi ne, sai ka kasance baka shaye-shaye, kafin ka iya yaƙar ɗabi’ar’‘.

Da ya ke gabatar da nasa jawabin kuwa, Shugaban ƙaramar hukumar Jalingo, Alhaji Jamo Hassan Mafindi, wanda ya samu wakilcin Daraktan Sashen Cibiyoyin Kula da Lafiya Matakin Farko, ce wa ya yi, shirin ya zo akan gaɓa duba da buƙatar da ke akwai ta dakatar da yin amfani da matasa, wajen tayar da tarzoma ko yin maguɗi, a ya yin zaɓukan da ke tafe.

Ya na mai cewa, ”A ya yin babban zaɓen da ke tafe, ina fatan dukkannin waɗanda su ka kai shekaru 18 zuwa sama, za su karɓi katinansu na din-din-din, tare da kaɗa ƙuri’un su.

Kuma ku tabbatar kun san inda kuka yi rijsta, da inda akwatunan zaɓukanku su ke, dan haka ku tabbatar kun karɓi katinan zaɓenku na din-din-din, domin zaɓar ƴan takarkarun da ku ke da muradi, ka da ku bari a baku kuɗaɗe ku zaɓi ƴan takarkarun da basu cancanta ba, muddin ku ka yi hakan kuwa, to kamar kun saryar da ƴancinku ne, na tsawon shekaru huɗu”.

Taron na kwana guda, da ƙungiyar Ceto Ɗaliban Jihar Taraba ta gudanar haɗin gwuiwa da hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, reshen jihar Taraba, ya yi duba ne, kan muhimmancin Ilimin yara mata, ga al’umma, tare da kakkaɓe shaye-shaye, a matsayin jigo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button