’Yan matan Katsina sun yiwa maza fintinkau a jarrabawar kammala sakandire ta 2021

Badamasi Lawal, kwamishinan ilimi na Katsina, ya ce dalibai mata sun yi fice fiye da takwarorinsu maza a jarabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka ta 2021 (WASSCE).

Mista Lawal ya bayyana haka ne a wajen bikin rufe makarantar koyar da yara mata (GEP-III) a hukumance a ranar Alhamis a Katsina. Ya kara da cewa hakan ya samu ne sakamakon jajircewar da gwamnati ta yi na karfafa wa ‘yan mata a jihar ta hanyar shirye-shiryen ilimi daban-daban.

A cewarsa, a shekarar 2021 dalibai 18,321 ne suka zana jarabawar WASSCE, kuma gwamnatin Katsina ta biya kudin jarabawar ga daukacin wadanda suka yi nasara.

“A cikin su 10,441 maza ne, yayin da dalibai mata 7,880. Amma abin mamaki, sakamakon ya nuna cewa 4,627 daga cikin dalibai mata ne suka samu maki a harshen Ingilishi, wanda ya kai kashi 58.7 cikin dari,” in ji Mista Lawal. “Daga cikin dalibai maza 10,441, 5,632 ne kawai suka sami maki a harshen Ingilishi, wanda shine kashi 54 cikin 100. Hakan na nufin ‘yan matan sun fi samarin maki a cikin harshen Ingilishi.”

A fannin ilmin lissafi, kwamishinan ya bayyana cewa ‘yan matan ma sun zarce samarin “saboda 5,678 daga cikinsu sun sami maki, yayin da 4,726 daga cikin mazan ne kawai suka samu maki” kuma “saboda yawan ‘yan matan da suka zana jarrabawar sun yi kasa da na dalibai maza, maza sun samu kashi 58 cikin 100 yayin da ‘yan matan suka samu kashi 53 cikin 100, wanda kuma ya fi haka.”

Mista Lawal ya kara da cewa, “Kiredit biyar da suka hada da Lissafi da Ingilishi a cikin adadin da aka ambata a sama, 4,247 daga cikin ‘yan matan ne suka samu kiredit, wato kashi 56 cikin 100, sabanin maza da suka samu kashi 48 kawai.”

A cewarsa, aikin na da nufin kara samun ilimi a tsakanin ‘ya’ya mata da kuma inganta kwazon malamai.

Ya kara da cewa duk ayyukan da aka ambata an cimma su a Katsina ta hanyar tallafin Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF).

“Ba shakka shiga tsakani ya inganta ilimin yara mata a jihar Katsina. Ina so in nuna shaidar wannan cigaba ta hanyar gabatar da sakamakon WASSCE na 2021, “in ji kwamishinan. “Zai nuna muku cewa kasancewar UNICEF a jihar ya yi matukar kyau wajen inganta ilimin yara mata.”

(NAN)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *