Ilimi

Ilmin Halittar Dan Tayi Da Annabi Muhammadu { S.A.W } Yazo Da Shi Ya Tabbatar Mana Da Gaskiyar Manzoncinsa – Farfes Keith L. More.

Spread the love

Farfesa Keith L. Moore PhD, DSc, FIAC, FRSM, FAAA, Bijimin malami ne kan ilmin surar ɗan Adam da kuma ilmin halittar Dan tayi a jami’ar Toronto, Canada. Farfesa Keith L Moore, ya yi rubuce-rubuce da gabatar da muƙaloli masu ɗumbun yawa a waɗannan fannoni.

Kuma zuzzurfan binciken da farfesan ya gudanar tsawon lokaci ya haifar da wallafa shahararren littafinsa kan ilmin hallittar tayi, wato ‘The Developing Human: Clinically Oriented Embryology’. Har i zuwa yau, wannan littafi ya fi kowane littafi a wannan fanni karɓuwa a ƙwalejojin koyar da likitanci a faɗin duniya.

A ƙoƙarin neman madogara da dalilai kan halittar tayi, farfesan ya kafa hujjoji da ayoyin ƙur’ani da suka yi bayani kan halittar ɗan Adam a cikin uwa.

Bayan wallafa wannan littafi kuma, ya gabatar da muƙalolin a tarukan kimiyya daban-daban inda yai ta bayyana yadda bayanan halitta ɗan Adam a cikin ƙur’ani suka yi cif da cif da binciken kimiyar zamani.

A wani taron ƙasa da ƙasa kan ilman kimiyya da ke cikin ƙur’ani da sunnah, wanda aka gudanar a ƙasar Masar a shehara ta 1989, Farfesa Keith L. Moore, ya gabatar da muƙala mai taken: “Abinda ƙur’ani ya ce kan halittar tayi”, inda kuma ya ƙarƙare muƙalar da cewa “ya kamata a riƙa amfani zangunan halittar ɗan Adam da ƙur’ani ya ambata wajen koyar da ɗalibai musulmi, saboda ya yi dai-dai da binciken zamani kan halittar ɗan Adam kafin haihuwa, kuma zai bai wa likitoci da malam jinya musulmi damar yi wa marasa lafiya bayani kan halittar ɗan Adam dogaro da ƙur’ani. Abu ne mawuyaci Annabi Muhammad (SAW) ya san ilmin halittar tayi tun a ƙarni na bakwai im ba hawayinsa aka yi masa ba, saboda mafi yawancin ilman har sai a ƙarni na 20 binciken kimiyya ya kai ga ganosu. Wannan ya tabbatar min ce wa, tabbas annabi Muhammad (SAW) jakadan Allah ne”.

Bugu da ƙari, farfesa Keith L. Moore ya yi ta maimaita wannan magana a laccoci da sauran tarukan kimiyya, wanda hakan ya janyo raɗe-raɗi kan musuluntarsa. Bayan yawaitar wannan raɗe-raɗi, an tambaye shi a bayyanar jama’a cewa ko ya musulunta, inda ya ce ya yi imani da Allah, kuma yana girmama sauran addinai, sai dai yana bauta masa ne daban da yadda musulmi ke yi kawai, kuma babu buƙatar dole sai ya musulunta kafin ya bauta masa.

Sai dai, duk da haka mutane sun ci gaba da cece-kuce kan tabbacin musuluncinsa, inda wasu ke ganin ya ɓoye musuluncinsa ne duk da bayanin da ya yi a bayyanar jama’a.

Daga Umar Gaya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button