Rahotanni

In Ka Dauki Fim Iskanci Iskanci Zai Tafi Dakai, In Sana’a Ka Daukeshi Sana’a Kakeyi, Inji Jaruma Fadila Muhammad A Hirarta Ta Karshe Kafin Ta Rasu.

Spread the love

Tattauanawar da Jaruma Fadila Muhammad tayi da sashin Hausa na Rediyo Faransa ita ce tattaunawar karshe da tayi da wata kafar yada Labarai.

Anyi tattaunawar ne kwanaki kadan kafin rasuwar jarumar, hakan tasa muka dan tsakuro muku kadan daga cikin abin da ta fada.

Jarumar tace “Fim sana’a ne, bazan iya misalta yadda na dauki fim ba, abin so ne sosai, ina kaunar fim”.

Ko da aka tambayeta game da yadda akai tafara fim, Jaruma Fadila Muhammad ta ce “Bazan iya cewa ga yaddaa nafara fim ba, amma dai kafin in fara fim Fati K.K kawata ce, Fati Ladan kuma makwabciyarmu ce. Fati Ladan tana zuwa gidanmu sai magulmata suke cewa mahaifina wai ina tara ‘yan fim suna cika a gidanmu, ni ban san ‘yan fim ba, Fati Ladan da Fati K.K kawai nasani, kuma ban taba binsu inda suke fim ba”.

Fadila ta cigaba Cewa “Tun ana fadawa mahaifina ba ya yadda, har wata rana yakirani yacemin ance masa an ganni a fim, nace masa ba ni bace, da aka saka fim din sai yaga Fati K.K, sai nace masa kama ne tazo daya amma ba ni bace, nace masa ya kalla sosai, kawai dai yanayinmu ne iri daya, gaskiya muna kama sosai da Fati K.K, kuma bamu hada komai da ita ba, kawai dai ita kawata ce sosai”.
Jarumar tace ” Bana sha’awar fim, Yayar babanmu ce da ta dage akan cewa wai na fara fim, sai nace to bari inyi fim din tun da ance ina yi. A gaskiya ban taba sha’awar yin fim ba, kuma ban taba raka wata wajen fim ba”.

Ta cigaba da cewa “Lokacin da zan fara fim na fadawa babana, ya yimin addu’a ya sakamin albarka. Farkon fara zuwana Location lokacin da Fati Ladan zatayi wani fim nata, sai tacemin mecece gudun mawata, sai nace addu’a, sai tace nazo nayi addu’ar, sai nace mata idan nayi sallah zanyi, sai ta dage dai sai naje, tayimin kwatance ban gane ba, ta turo aka daukeni. Na ga Jarumai irin su Shu’aibu Kumurci a wajen, da su Lawan Ahmad da sauransu. Akayi wasa da dariya, abin ya yimin dadi, sai nace gobe zan dawo.

Fadila tace “Lokacin da zan fara fim iyayena sun gargadeni da na tabbatar da tarbiyar da suka bani, sannan kuma na tabbatar da cewa na yi makarantar Islamiyya na yi sauka na yi hadda, sannan kuma na tsaya a turbar addinin Musulunci”.

Jarumar wadda ta shafe shekaru 8 a masana’antar shirya fina-finai ta kannywood ta fara fitowa ne a wani fim mai suna Sama Da Nisa na Nazifi Asnanic, daga shi sai ta haska a cikin fim din Kamfanin Adam A Zango na Hubbin So, daga shi sai Basaja, daga shi sai Aliya, daga shi sai Gidan Dadi.

Jarumar tace “Wani lokacin mutane ba sa yimana uzuri, wani lokaci mutane zasu kiramu a waya bamu sami lokacin dagawa ba sai suce mu ‘yan wulakanci ne, ba sa duba irin uzurin da ya hanamu daga wayar tasu. Sannan kuma mutanen unguwa da zaran kin fara fim sai ayita cewa ai wance ‘yar iska ce, ta fara fim da sauransu, in ka dauki fim iskanci iskanci zai tafi dakai, in sana’a ka daukeshi sana’a kakeyi, to mu mun daukeshi sana’a, kuma Alhamdulillahi babu abin da zamuce da Allah sai godiya”.

Jarumar ta kara da cewa “Akwai mazajen da za su nemeki da aure, amma a unguwarku sai mutane suyita cewa ai wance ‘yar fim ce, ai kaza da kaza, idan dama da karya yazo ba auren yazo ba, ba zai dawo ba, idan kuma da yaudara yazo zai dawo, amma ba maganar aure zaiyi miki ba, sai dai yayi miki wata magana ta daban.

Wannan kadan kenan daga cikin tattaunawar jaruma Fadila Muhammad da sashen Hausa na Rediyo Faransa Kwanaki kadan kafin Rasuwarta.

Muna Fatan Allah Yayi Mata Rahama, Amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button