Ina Ƙoƙarin Kiyaye Mutuncina Sabida Na San Gidan Dana Fito Gidan Sarauta Ne, Inji Jarumi Ibrahim Sabon Yayi.
Jarumin ya ce “Ni Furodusa (producer) Ne, kuma Jarumi ne sannan mawaƙi a masana’antar shirya fina finan Hausa ta kannywood.”
An haifi Jarumi Ibrahim Sabon yyayi a Jihar Kaduna cikin Ƙaramar Hukumar Birnin gwari, ya yi karatun firamare (primary) a Jibril Mai Gwari primary school, daga nan ya tafi Government Junior secondary School Birnin Gwari, ya ƙarasa karatunsa a Mamman kwantagora Technical College Pandogari Jihar Neja (Niger State) Inda ya karanci Fasahar wutar Lantar ki (Electrical).
Jarumin ya samu Takardan shaidar (Nabteb), Bayan nan ya ci gaba da karatunsa a kaduna, Inda yayi Difiloma (Diploma) A Fannin kimiyar Na’ura mai ƙwaƙwalwa (Computer science), A Staff Development Center Kakuri kaduna, inda yanzu ta koma Reshe na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).
Jarumi Ibrahim Sabon Yayi ya ce “Na shiga Sana’ar waƙa da Fim tun ina aji uku na Babbar Sakandire (SS 3), kuma a ƙalla yanzu na kai shekara Goma sha uku ina masana’antar.”
“Amma saboda yanayin Harkoki da kuma abubuwa na yau da kullum a lokacin bayan nayi wasu Fina Finai guda huɗu, Bado, da Tulu, da So Mai Saƙa, da Waye Isasshe.”
Daga nan sai kuma Jarumin ya koma makaranta saboda ƙaro Ilimi.
Ibrahim Sabon Yayi ya ce “Alhamdulillah, bayan ɗaukan lokuta muna mummurza Al’amura na Rayuwa, da yake Ina harkokin siyasa sosai kuma muna waƙoƙin siyasa dai dai Gwargodo.”
“Ana haka a wannan ƙarni da kuma na dawo sai nayi ma kamfanin mu Rijista (Register) mai Suna One Family Film Production, Wanda muke jagoranta dani da Abokina kuma mai daukar Nauyin Fim sabon Jarumi kuma Anas Idris Ɗan Alhaji, Yanzu haka munyi Fina Finai guda shida a kamfanin mu, daga dawo warmu A shekara ta dubu biyu da sha tara wato 2019.”
Fina-finan sune kamar haka:-
-Managarcin Namiji wanda Bashir Nayaya da Salisu S Fulani dani muka Jagoranta.
- Mummunar Kishi
- Raliya Adam A Zango da Rikadawa sune manƴan Jarumai a fim ɗin.
- Jigon Rayuwa wanda ƴan wasa kusan talatin suke cikin Fim ɗin, Anas Ɗan Alhaji ya ɗauki nauyi.
- Amrah
- Ashababu Uƙdud,
Waɗannan sune Fina Finai na kamfanin mu bayan dawo warmu, kuma guda biyu suna kasuwa, Jigon Rayuwa, da Raliya, sauran kuma suna Hanƴa.”
Jarumin ya cigaba da cewa “Dukkan Abokan Sana’ata muna mutunta juna kuma babu wanda ya tsare mani a gaba, a matsayin wanda zai bani matsala a Rayuwata.”
“Ina ƙoƙarin kiyaye mutunci na saboda na san gidan da na fito Gida ne mai Daraja na Masarauta, shiyasa nake ƙoƙarin Kiyaye hurɗa ta da Jama’a.”
“Muna roƙon Allah ya bamu dacewa yakuma yi mana jagora akan lamarin Rayuwa yasa mana Albarka a cikinta.”
Daga Karshe Jarumin ya ce “Masoya na ina Alfahari daku ta yadda nake ganin saƙonnin ku da kuma goyon baya da kuke bamu, muna Roƙon Allah ya bamu nasara a Rayuwar mu Gaba ki daya Amiin.”