Siyasa

Ina Abba Gida Gida?

Spread the love

Sarkin Farin jinin siyasa ko ina ya shiga ne?

Eng Abba Kabir Yusuf shine yayima Jam’iyar PDP takarar gwamna a shekarar 2019 karkashin kungiyarsu ta Kwankwasiyya Shine ake kira da abba gida gida Shine dan siyasa kwaya daya tal daya samu daukaka yafi ko wanne dan siyasa farin jinin siyasa cikin Karamin Lokaci aduk yankin Africa yayi takara da tsohon dan siyasa kuma Gwamna me rike da madafun iko amma duk da hakaz a zabe na farko kafin a dage zaben sai da abba gida gida yayima Gwamna tazarar Kuri’u masu tarin yawa gasu kamar hakaa malam Abba gida Gida Ya Samu Kuri’u 1,014.474 yayinda shi kuma gwamna ganduje ya samu Kuri’u 987,819 hakan ya nuna abba gida gida ya cinye zaben Gwamnan a zagayen farko…

Sai dai a zabe na biyu Gwamna Ganduje ya samu nasara kan abba gida gida da Kuri’u 1,033,695 yayinda shi kuma abba ya samu Kuri’u 1,024,713 hakan ya nuna ganduje shine Yayi nasara kan abba gida da kyar kamar yadda hukumar zaben Nageriya INEC ta bayyana…

Wasu na ganin farin jinin abba gida bashi rasa nasa ba ga farin jinin mai gidansa ga al’umma na soyayya da suke masa haka yasa shima abba gida ya samu wani sashi na wannan soyayya ta farin jini wato Soyayyar al’umma ga Eng Rabi’u musa Kwankwaso tsohon Gwamnan jiharta Kano..

Tun bayan da kotun kolin Nageriya ta bayyana samun nasarar gwamna Ganduje shikenan ba’a sakejin duriyar malam abba gida gida ba sai a kwana kwanan nan da akajiyo sakon muryarsa na jajantawa ga al’umma kan batun COVID19…

Mutane da dama suna yawan tambaya kan cewa ko ina abba gida gida ya shiga shine muma anan gidan jaridar mikiya muke Tambaya shin ina abba gida gida??

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button