Wasanni

Ina jin tsoro, Allah ya kiyaye ni – Dan wasan Al-Hilal yayi magana akan zuwan Messi kulob din na Saudi Arabia

Spread the love

Dan wasan baya na Al-Hilal, Ali Al-Bulaihi ya yi raha cewa yana tsoron korarsa idan Lionel Messi wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai ya isa kulob din Saudiyya.

Al-Bulaihi, wanda yake son Allah ya kare shi, ya kuma ce zai buya ne don gudun kar a samu korar Al-Hilal saboda Messi.

An danganta Messi da komawa Al-Hilal a bazara saboda kwantiraginsa a Paris Saint-Germain zai kare a bazara.

An yi wa dan wasan mai shekaru 35 tayin zunzurutun kudi har Yuro miliyan 500 duk shekara domin ya koma Al-Hilal daga PSG.

Da yake magana da SBC, Al-Bulaihi ya ce: “Ban san abin da zai faru ba, kuma ina tsoron kada shi [Lionel Messi] ya ce, ‘Ba na son lamba biyar.’

“Ban sani ba ko Messi zai zo ko a’a, amma idan ya zo [ga Al-Hilal], Allah ya kiyaye ni! Idan ya zo in sha Allahu, ba zan halarci kwana biyun farko ba, sai na sa ido daga nesa don ya manta da ni”.

Idan har Messi ya koma Al-Hilal, to hakan zai sa ya fuskanci abokin hamayyarsa na dindindin, Cristiano Ronaldo, wanda a halin yanzu yake bugawa kungiyar Al-Nassr a gasar Saudi Pro League.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button