Ina Jiyewa Shugaba Buhari Tsoron Kamun Da Allah Zai Yi Masa, Saboda Tsaron Nan Dai Shi Yayi Alkawarin Kawo Shi Inji Dr. Naja’atu Bala Muhammad.
Matsalar Tsaro: Hajiya Naja’atu Ta Bara
Shahararriyar ‘Yar siyasarnan, Hajiya Naja’atu Bala Muhammad ta nuna takaicinta akan yadda matsalar tsaro ta dabaibaye Arewacin Najeriya.
Hajiya Naja’atu Bala Ta ce
“Duk sanda za kaji labarin tsaro a Najeria, to wallahi tallahi a Jarida ne kawai, amma banda a zahiri, kuma.”
Hajiya Naja’atu ta kara da cewa “Ina jiyewa shugaba Buhari tsoron kamun da Allah zai yi Masa, saboda tsaron nan dai shine yadauki alkawarin kawo shi, saboda yadda ya ringa dora alhakin rashin tsaron akan tsoffin shugabannin baya.”
Hajiya Naja’atu ta ce “Amma yanzu kamar ba shi bane yake sukan tsohuwar gwamnati akan tsaron ba, ya yiwa al’ummar Najeriya alkawarin samar musu da cikakken tsaro, ya je ya shantake a Abuja cikin Villa.” Inji Dr Naja’atu bala Muhammad.
Daga Kabiru Ado Muhd