Rahotanni

Ina Kira ga Gwamnatin tarayya data hada Kai da Gwamnatin jihar kaduna domin yaki da ta’addancin Hanyar kaduna Abuja ~Inji Sanata Uba Sani..

Spread the love

Sanata Uba Sani Ya yii Allah Wadai da Sababbin hare-hare kan al’ummomin kananan hukumomin Igabi da Kajuru, da kuma hanyar Kaduna zuwa Abuja sanatan Yace abin damuwa ne kuma abin Allah wadai ne. Wadanda ba ‘yan jihar ba, tare da samun damar amfani da kayan tashin hankali, suna aiki cikinsu sauki dole ne ya zama abin damuwa ga duk mai sha’awar tsaro da son jin dadin mutanenmu.

Sun afkawa kauyen Albasu dake karamar hukumar Igabi. Sun yi barna sosai a Maraban Kajuru dake Karamar Hukumar Kajuru. Haka Kuma a hanyar Kaduna zuwa Abuja suka kwashi wasu mutane, ciki har da daliban jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

Ci gaba da kawanya da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da ‘yan fashin suka yi, cin fuska ne kai tsaye ga Gwamnatin Tarayya musamman jami’an tsaro. Masu aikata Miyagun laifuka lallai ba za su samu galabar samun hanyar shigowa cikin ƙasarmu ba kuma ace mun kasa ɗaukar tsauraran matakai. Wannan lokaci ne da ya kamata muyi yaki da ‘yan fashi da masu satar mutane tare da tabbatar da Gwamnatin Tarayya ta mallaki kayan aikin tilastawa ga jihohi.

Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hada hannu da Gwamnatin Jihar Kaduna don tumbuke wadannan ‘yan fashi daga kananan hukumomin Igabi da Kajuru. Haka nan ya kamata Gwamnatin Tarayya ta gudanar da wani samame na tsawon wata guda a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja don kaskantar da ‘yan fashin da masu satar mutane Kan Kowa, komai girman matsayinsa, da aka gano yana taimakawa da aikata laifuka a hanyar ya kamata a hukunta shi. Dole ne al’ummomin da ke kan babbar hanyar su kasance cikin aikin sa’ido

Ina mika ta’aziyyata ga dangin wadanda suka rasa ‘yan uwansu a hare-haren Muna masu fatan Samun salama. Ina kuma yin addu’ar Allah Ya dawo da daliban nan 8 na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da sauran ’yan Najeriya marasa laifi wadanda aka yi garkuwa da su a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Da fatan Allah Madaukakin Sarki Ya karfafe su yayin da suke cikin wannan mummunan halin. Sanata Uba Sani

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button