Rahotanni

Ina Kira Ga sabon mahaifinmu Sarkin Zazzau Daya gudanar da mulkin sama da na marigayi Sarki Shehu Idris~ Sanata Uba Sani.

Spread the love

Jim kadan A jiya bayan Mika Sandar Mulki ga sabon Sarkin na Zazzau da Malam Nasir El-Rufai ya gudanar Sanata Uba Sani ya wallafa tare hotuna a shafinsa na Twitter Yana Mai cewa A safiyar yau, na bi sahun Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai da sauran manyan mutane na kasance a wajen bikin nadin Mika Sandar ga sabon Sarkin Zazzau, HRH Ahmed Nuhu Bamalli.

Bikin Daya kasance mai kayatarwa shine cikamakin bincike mai zurfin gaske don neman magajin Shehu Shahararre (mai tarin albarka).

Ina yabawa mai girma Gwamnanmu, Malam Nasir El-Rufai daya bai wa mutanen Masarautar Zazzau sarauta mai martaba da kima. Har ‘ila yau Kuma Ina kira ga sabon Mahaifinmu da ya gudanar da mulki gami da kokarin zarcewa bisa cancanta na marigayi HRH Shehu Idris.

Ina yin kira ga mutanen kirkin nan na masarautar Zazzau da su ba sabon Sarkin duk wani goyon bayan da ake bukata don taimaka masa wajen gudanar da aikinsa na ciyar da masarautar zuwa manyan matakai.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ba HRH Ahmed Nuhu Bamalli hikima da fahimta don jagorantar mutanen kirki na Masarautar Zazzau. Ina yi masa fatan samun nasara da zaman lafiya.

Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button