Labarai

Ina lakadawa matata dukan tsiya ne domin na bata tarbiyya tare da ‘ya ‘ya na wani magidanci ya Fa’dawa Kotu a kaduna.

Spread the love

Wani magidanci mai ‘ya’ya hudu, Lukman Soladoye, a ranar Talata, ya gurfana a gaban wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna bisa laifin dukan matarsa, Kemi Soladoye da ‘ya’yansu hudu.

Soladoye ya ce ya lakadawa matarsa ​​da ’ya’yansa duka domin ya gyara musu a lokacin da suka yi kuskure inda ya ce yana kaunar iyalinsa kuma yana son alheri a gare su.

Tun da farko dai mai shigar da karar ta bakin lauyanta B. A Tanko ta ce ta na son a raba auren ne saboda cin zarafi da ake yi mata amma daga baya ta sauya ra’ayinta ta sasanta da mijinta.

Ta roki kotu da ta ja kunnen wanda ake kara da ya daina cin zarafinta da ‘ya’yansu.

Alkalin kotun Malam Isiyaku Abdulrahman ya tambayi wanda ake kara ko zai yi alkawarin daina dukan matarsa ​​da ‘ya’yansa, shi kuma wanda ake kara ya ce zai daina dukan matar, Amma ba ‘ya’yansa ba.

“Idan matarka ta yi maka wani laifi, ka yi magana da ita kuma ka nuna bacin ranka; bai kamata ka doke matarka ba.

Amma ga ’ya’yanku, ba duka ba ne kawai hanyar gyara yaro; Ku rika nuna soyayya da kauna ga ‘ya’yanku, ku yi musu addu’a, ku yi masu nasiha,” inji alkalin.

Alkalin kotun ya ce kotun za ta ci gaba da sanya ido kan halayen wanda ake karar sannan ya bukaci mai karar da ya kai kara kotu idan wanda ake kara ya sake kai mata hari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button