Ina mai farin cikin sanar da cewa, wadanda suka ci gajiyar shirin Survival Mutum 101,567, wadanda aka debo daga kamfanoni 16,253 a yau sun karbi biyan su na wata ~ Shugaba Buhari
Biyo bayan nasarar tantance wadanda suka nemi aikin, Gwamnatin Tarayya ta ce ta biya ma’aikata 101,567 da aka tantance wadanda aka zabo daga kamfanoni 16,250 a karkashin shirinta na tallafa wa masu biyan albashi (MSME Survival Fund) don kananan ‘yan kasuwa, in ji Brainnews.
Gwamnatin Tarayya za ta tallafawa kananan ‘yan kasuwa don biyan bukatunsu na biyan albashi tsakanin N30,000 zuwa N50,000 don magance tasirin tattalin arziki na cutar Covid-19.
Matsakaicin ma’aikata 10 za’a biya a tsawon watanni 3.
A shafin twitter na Shugaba Muhammadu Buhari, an Rubuta:
“Ina mai farin cikin sanar da cewa, wadanda suka ci gajiyar shirin su 101,567, wadanda aka debo daga kamfanoni 16,253 a yau sun karbi biyan su na wata-wata daga shirin Tallafin Biyan mu. Shirin @SurvivalFund_ng don taimako don tallafawa MSMEs masu cancanta tare da albashin ma’aikata na watanni 3.