Labarai

Ina neman afuwar azabar da manufofina suka jawo wa ‘yan Najeriya, inji Buhari

Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi afuwa kan illar da manufofinsa na tattalin arziki ke yi ga ‘yan Najeriya.

Shugaban a jawabin bankwana da ya yi a ranar Lahadi, ya ce an yanke shawarar ne domin amfanin kasar.

Shugaban ya ce ya ji dadin yadda gwamnatin sa ta fara sake haifuwar Najeriya ta hanyar daukar muhimman matakai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga al’ummar kasar a wani shirin bankwana da aka yi da safiyar Lahadi, kwana daya kafin ya sauka daga mulki.

A jawabin, shugaban ya bayyana godiyarsa ga ‘yan Najeriya, ya kuma bayyana tunanin wasu muhimman shawarwarin da gwamnatinsa ta yanke, ya kuma bayyana imaninsa cewa zai bar kasar fiye da yadda ya gamu da ita.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button