Wasanni

Ina Son Na Koma Barcelona, Ronald Koeman Ya Sanar Da Kungiyar KNVB.

Spread the love

Rahotanni sun ce shugabannin Barcelona na tattaunawa da hukumar kwallon Holland (KNVB) yayin da suke kokarin nada Ronald Koeman a matsayin sabon kocin kungiyar.

Quique Setien ya sauke aikinsa ranar Litinin da yamma bayan wani taro tsakanin kwamitin gudanarwar Barcelona a Camp Nou. Koeman a yanzu shi ne kocin Netherlands, amma a baya ya bayyana cewa akwai wani batun musamman a kwantaraginsa da zai ba shi damar rike mukamin na Barcelona.

Wannan kwantaragin an kulla shi ne bayan Euro 2020, amma jinkirta wajan wancan gasa da kuma rashin tabbas game da kwallon kafa na kasa da kasa yana nuna cewa yakamata ya iya jan ragamar Camp Nou a yanzu.

A ranar Lahadin da ta gabata, an hango Koeman a filin jirgin sama na Barcelona, ​​inda yake tashi zuwa gida Netherlands saboda tuni ya tattauna da Barcelona.

Tsohon dan wasan na Blaugrana ya kasance mai yiwuwa ne ya dawo gida kasarsa don tattaunawa kan ficewar sa daga kungiyar KNVB.

Kamar yadda kamfanin dillancin labaran Holland ya ruwaito, Koeman ya fada ma kungiyar ta KNVB cewa yana son ya koma Barcelona.

Rahotanni daga Voetbal sun kuma ce wakilan Barcelona suna kasar don gudanar da tattaunawa da kungiyar ta KNVB.

Voetbal ta kara da cewa tsohon kocin Hoffenheim Alfred Schreuder zai koma Camp Nou a matsayin mataimakin Koeman.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button