Kasashen Ketare

Ingila Ta Yi Barazanar Kwace Kadarorin Duk Wadanda Suka Sake Sukayi Magudi A Zaben Edo Na Kasashen Waje.

Spread the love

A wata sanarwa da ofishin jakadancin Burtaniya da ke Najeriya ya fitar yau talata, ya ce kwace kadarorin irin wadannan mutanen a kasashen waje zai iya Ingaganta Damokuradiyya a kasarnan.

Zabukan Najeriya galibi suna cike da rikici ta hanyar satar akwati da kwace kayayyakin zabe, kamar yadda lamarin ya kasance a zabukan baya-bayan nan a jihohin Kogi da Bayelsa.

A cikin wata sanarwa a shafin Twitter, Burtaniya ta ce za ta tura masu sa ido kan zaben da ke tafe a jihohin biyu.

“A matsayin kawa kuma abokiyar tarayyar Najeriya muna bin kadin yadda aka gudanar da zaben fitar da gwani a jihohin Edo da Ondo da aka shirya a ranar 19 ga Satumba da 10 ga Oktoba 10,” in ji shi.

“Wadannan zabubbukan suna da mahimmanci, zamu dauki wadannan matakan ne domin samarda shugabanci nagari a tsakanin jihohin biyu da kuma manuniya ga karfin cibiyoyin dimokiradiyyar Najeriya.

“Za mu tura wakilan sa ido zuwa ga zaben Edo da Ondo da kuma tallafawa kungiyoyin fararen hula da zasu jagoranci sa idon a lokacin zaben.

“Burtaniya ta dauki mataki sosai a kan tashe-tashen hankula masu nasaba da zabe, kuma, kamar yadda muka yi a babban zabe a shekarar 2019, za ta ci gaba da daukar mataki a kan mutanen da muka gano suna da alhakin tashin hankali a lokacin zaben.

“Wannan na iya hadawa da takaita cancantar su zuwa Ingila, takaita samun damar mallakar kadarorin Burtaniya ko gurfanar da su a karkashin dokar kasa da kasa.

“Kasar Burtaniya za ta ba da goyon baya da hadin kai yayin da muke tunkarar wadannan zabuka. Muna kira ga INEC, ‘yan sanda da duk sauran hukumomin da abin ya shafa da su yi aiki tare don gabatar da zabe na gaskiya da adalci.”

Kwamishiniyar Burtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ta gana da shugabannin jam’iyyun (APC) da na (PDP) yayin da ta yi kira da a gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba.

“Tattaunawar ta mayar da hankali kan bukatar shugabannin jam’iyyun su yi galaba a kan magoya bayansu don kaucewa tashin hankali kafin da bayan zaben,” in ji sanarwar.

“Kuma muna maraba da sa hannun ‘yan takarar Edo na kwamitin zaman lafiya na kasa da INEC suka shirya yarjejeniyar zaman lafiya.”

Gargadin daga Burtaniya na zuwa ne kwana guda bayan da Amurka ta sanya dokar hana biza ga mutanen da suka yi kafar ungulu ga zaben gwamnoni da aka yi kwanan nan.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button