Siyasa

Inyamurai ne ya kamata a baiwa mulkin kasar nan a 2023, Cewar Kungiyar Dattawan Arewa.

Spread the love

Wata kungiyar dattawan Arewa dake neman hadin kai da zaman lafiya ta bayyana cewa a shekarar 2023 dan Kudu daga kabilar Inyamurai ya kamata abaiwa dama yayi mulkin Najeriya.

Kungiyar ta bayyana hakane ta bakin shuwagabannin ta, Zanna Goni da kuma shugabar bangaren Mata, Hajiya Mairo Bichi, kamar yands Vanguard ta ruwaito.

Kungiyar tace a yanzu tunda shugaba Buhari dan Arewa ne, abinda ya kamata shine a baiwa dan kudu kuma Inyamuri dama ya zama shugaban kasa a shekarar 2023.

Tace tana kira ga dukkan jam’iyyun Siyasar kasarnan a shekarar 2023 su tsayar da dan takara da kabilar Inyamurai sannan kuma ‘yan Najeriya su bada hadin kai.

Ta kara da cewa wannan zai taimaka wajan rage yawan kukan da Inyamurai ke yi na cewa ana nuna musu wariya a Najeriya. Ta kara da cewa, kuma tana jinjinawa shuwagabannin inyamurai da basu nuna goyon baya akan kungiyar IPOB ba.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button