IPMAN Ta Zargi NNPC Da Gaza Aiwatar Da Rage Farashin Man Fetur Din Da Ta Bayyana Cewar Tayi.

Daga Miftahu Ahmad Panda
Kungiyar Masu Sayar Da Manfetur Ta Kasa IPMAN Reshen Jihar Kano, Ta Zargi Kamfanin Mai Na Kasa NNPC Da Gaza Aiwatar Da Rage Kudin Manfetur Din Da tayi, Biyo Bayan Faduwar Farashin Man Fetur Din a Kasuwar Mai Ta Duniya, Bisa Barkewar Annobar COVID – 19 a Mafi Yawan Kasashen Duniya
Shugaban Kungiyar a Jihar Kano, Alhaji Bashir Dan Mallam ne ya Bayyana Hakan a Lokacin Da yake Zantawa Da Manema Labarai a Jiya Talata,
Haka Zalika Dan Mallam ya Zargi Shugaban Kamfanin Na NNPC Mallam Mele Kyari, Da kuma Wasu Daga Cikin Shuwagabannin Kamfanin Da Rashin Daukar Matakan Da zasu Farfado Da Tattalin Arzikin Kasarnan Daga Halin Mashashsharar Da yake Neman Afkawa Tare da Zama ‘Yan Babu Ruwanmu Musamman ma a Bangarensu Na Manfetur.
A Karshe Bashir Dan Mallam ya Bukaci Sauran Shuwagabanni Tare da Membobin Kungiyar da suke a Jihar Kano da kuma Sauran Jihohin Kasarnan dasu tabbatar Da cewar Ana Cigaba da Dakon Manfetur Zuwa Dukkannin wasu Sassan Kasarnan Da Ake Bukatarsa Domin Gudun Gazawarsa.
Domin kuwa a Duk Lokacin Da Aka Samu Karancin Manfetur to kuwa Babu Shakka Al -amuran Yau Da Kullum sukan ta’azzara a Shiga Kuncin Rayuwa, Dafatan Allah ya Karemu.