Tsaro
IS Tayi ikirarin Kashe Civilian JTF 90 a jahar Borno.

A jiya Juma’a ne Kungiyar nan dake Ikirarin kafa daular musulunci a Arewa maso gabashin Kasar nan IS Ta wallafa a shafinta cewar ita takai Mummunan Harin nan Garin Foduma dake karamar hukumar Gubio ta jahar Borno Inda tace ta kashe mayakan sakai guda 90.
Idan baku mantaba Harinda Kungiyar take ikirarin takai shine wanda yaja Hankalin Al’ummar kasar nan a Cikin makonda yagabata Inda ake Cewa Boko haram ta kashe Mutane 81 a Jagar Borno.
Daga Ahmed T. Adam Bagas