Fashion

Ita ce Macen datafi kowa tsawon Farce a Duniya.

Spread the love

Ayanna Williams ƴar asalin ƙasar Amurka ita ce ta shiga kundin adana abubuwan tarihi na duniya wato Guinness World Records a shekarar 2008 a matsayin wacce tafi kowa tsawon farce a duniya.

Tsawon farcenta ya kai mita 5 da rabi sannan ta kwaso shekaru 23 tana tara shi.

Ayanna William a loƙacin da take tattaunawa da ƴan jarida ta bayyana cewa babban ƙalubalen da take fuskanta da tara farcen shine tana ɗaukar loƙaci mai tsawo kafin ta yi wasu aikace-aikacen na tsakar gida.

Ta ƙara da cewa tana ɗaukar tsawon sati guda tana yiwa farcen nata ado domin ya ƙayatar da masu kallonsa.

Bugu da ƙari tana siyo turare kala-kala domin ta yiwa farcen nata kwalliya.

Daga Mutawakkil Gambo Doko.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button