Uncategorized

Jagoran juyin mulkin Nijar bayan ya gana da malaman addinin Musulunci na Najeriya, ya ce kofa a bude take domin tattaunawar sulhu

Spread the love

Abdourahmane Tchiani, shugaban mulkin sojan Nijar, ya ce sojoji a shirye suke su fuskanci tattaunawar diflomasiyya.

Tchiani ya yi magana ne a ranar Asabar yayin ganawa da tawagar shiga tsakani ta Najeriya da ta kunshi malaman addinin Musulunci.

Malaman addinin Islama karkashin jagorancin Bala Lau, shugaban kungiyar Jama’atul Izalatu Bida Waikamatu Sunnah na kasa, sun gana da Tchiani na tsawon sa’o’i a Yamai babban birnin kasar Nijar.

A cewar wata sanarwa da Lau ya sanyawa hannu a ranar Lahadin da ta gabata, jagoran juyin mulkin da malaman addinin Islama sun tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da bukatar shugabannin ECOWAS na a maido da tsohon shugaban kasar Bazoum.

Lau ya ce malaman addinin sun je Nijar ne a madadin shugaban kasa Bola Tinubu wanda ya amince da bukatarsu ta sa baki.

Don haka ya shaidawa Janar Tchiani cewa ziyarar ta Nijar na da nufin yin tattaunawa mai ma’ana don karfafa shi da sauran shugabannin sojojin da suka yi juyin mulki su bi tafarkin zaman lafiya a maimakon yaki don magance rikicin.

Da yake mayar da martani, Tchiani ya ce kofofinsu a bude suke don nazarin diflomasiyya da zaman lafiya wajen warware matsalar.

Ya kara da cewa, abin takaici ne yadda kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ba ta ji ta bakin gwamnatin mulkin sojan kasar ba kafin ta fitar da sanarwar.

Ya ce juyin mulkin an yi shi da niyya mai kyau, domin ana so a kawar da barazanar da ke tafe da ita da ba jamhuriyar Nijar kadai ba, har ma da Najeriya.

Ya kuma ba da hakuri bisa rashin kulawar da tawagar da shugaba Tinubu ya aika, karkashin jagorancin Abdulsalami Abubakar, tsohon shugaban kasa. Ya kara da cewa sun fusata ne sakamakon wa’adin da kungiyar ta ECOWAS ta yi.

Da manema labarai suka tambaye shi ko gwamnatin mulkin sojan a shirye take don tattaunawa, Ali Mahamane Lamine Zeine, firaministan Nijar, wanda gwamnatin mulkin soja ta nada, ya ce: “Eh, tabbas. Haka dai shugaban kasarmu ya gaya musu, bai ce ba ya son tattaunawa”.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa za a yi tattaunawa da ECOWAS nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

“Mun amince kuma shugaban kasarmu ya ba da haske kan tattaunawa. Yanzu za su koma su sanar da shugaban Najeriya abin da suka ji daga gare mu…. muna fatan nan da kwanaki masu zuwa, su (ECOWAS) za su zo nan su gana da mu don tattauna yadda za a dage takunkumin da aka kakaba mana,” inji shi.

Firaministan ya kuma ce takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakabawa “rashin adalci ne” kuma ya sabawa ka’idojin kungiyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button