Jama’a Sun Fara Guduwa Domin Tseratar Da kauyukansu A Neja.

Daga Ahmed T. Adam Bagas
Da yammacin Yau Lahadi ne Mazauna Kauyukan:- Nasa, Iburo, Galapai, Lagado da Sauransu Dake Karamar Hukumar Shiroro ta Jahar Neja Suke ta Kwarara Garin Zumba Domin Neman Mafaka.
Masu gudun Hijiran Suna Tsallakowa Ta Hayin Ruwa suna Shiga garin Zumba Domin Tsira da Rayuwar su.

Mazauna Kauyukan Sun yanke shawarar Barin Garinsu Ne bayan wani Hari da yan Bindiga Suka kai Yankinsu Ranar Juma’a da tagabata Inda aka Kashe mutum 1 aka Kore shanu 150 a Kauyuka makobtansu Dake Karamar Hukumar Shiroro Ta Jahar Neja.

Sunce barin garuruwan nasu Shine mafita garesu, Wani mutum Wanda ya nemi asakaye Sunansa Ya Shaidawa MIKIYA Cewa dole ne Su gudu su tsira da Rayuwarsu tunda Gwamnati tayi Biris Ana kashesu:- Inji Su
A kwanakin Baya ma Sanatan yankin Da abin ya Ke faruwa Sanata Sani Musa 313 ya Kai wannan koken sa gaban Majalisa da Zummar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya Kafa San sanin Soji a yankin domin dakile Aikin yan Ta’adda a yankin, Kuma sanatan ya gana kai tsaye da Shugaba Buhari, amma Har tanzu Ba’a yi Abinda ya dace a Yankin ba.
Sai dai a Ranar Alhamis dinda ta gabata Gwamnan Jahar Abubakar Sani Bello ya Tabbatar wa Al’ummar Jahar suyi Hakuri Za’a dauki matakan Dakile Aikin Ta’addanci a Fadin Jahar.
Gwamnan ya Sanarda hakan bayan ya gana da Kwamandojin Tsaron Jahar a Fadar Gwamnatin Jahar.
Allah ya kawo mana Zaman Lafiya.