Jama’ar Gari Sun Farwa ‘Yan Bindiga A Katsina.
A Daren Juma’ar da ta gabata ne Yan Bindiga Masu satar Shanu suka Dira Garin Unguwar Gizo Dake Karamar Hukumar Faskari ta Jahar Katsina Inda Yan gari sukayi Fito na Fito da Barayin domin kare Dukiyarsu Nan da nan Barayin Suka Kashe Mutane 13 Suka Raunata 7 a Wannan Farmakin.
Kakakin Rundunar Yan sandan Jahar katsina Gambo Isah ya tabbatar da Aukuwar Lamarin Inda Isah yace Ganganci ne Yan Gari suyi Gaba da Gaba da Barayin da ke Dauke da Manyan Makamai Hadda AK47 Inji shi.
Yace Al’umma Su dinga Sanar da Jami’an Tsaro memakon Fito na fito da Barayi masu Dauke da manyan Bindigu Kukuma Kuna Dauke da Bindigar Harba Ruga.
Jahar Katsina dai Tayi Kaurin Suna wajen Ta’addacin Yan Bindiga Wanda Hakan Yasa Shugaban Kasa ya Umarci Jami’an Sojin Najeria dasu Gaggauta kawo karshen Aikin Yan Ta’adda a Yankin.