Jama’ar Kano sunci kudin BIL din wutar Lantarki Har Bilyan 17.589 ~KEDCO.
Gudanarwar Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya ce har yanzu ba a karbo sama da Naira biliyan 17.589 daga kwastomominsa tsakanin watan Janairu zuwa Disamba, 2020 ba.
A cewar wata sanarwa daga Shugaban, Kamfanin Sadarwa na Kamfanin, KEDCO, Ibrahim Sani Shawai, ya ce kudaden da ba a karba ba sun kasance ne sakamakon rashin biyan kudin.
Kamfanin na DisCo ya ce idan har aka warware wannan makudan kudaden, za a samu ingantacciyar hanyar bayar da aiyuka ta bangaren rarraba wutan cikin maslaha ga kwastomomi.
Ya yi kira ga kwastomomin da su biya kudaden da suka rage.
MD / Shugaba na KEDCO, Dokta Jamil Isyaku Gwamna ya ce “Muna cikin kasuwanci kuma muna da hisabi ga sauran abokan hulda da kudi kuma tsammanin KEDCO daga kasuwa ya kai kashi dari bisa dari.”