Labarai

Jami’an Hukumar ‘Yan sanda sun Harbe Wasu Masu Satar Mutane biyu a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Spread the love

Rahotani daga Abuja, babban birnin tarayya na cewa rundunar ‘Yanda sandan birnin sunyi nasarar kashe wasu masu satan mutane 2, tare da damke mutum 5 ‘yan kungiyar asiri, da wasu ‘yan fashi da ke addabar al’ummomin yankin Abaji na Babban Birnin Tarayyan.

An kashe masu satan mutanen ne da safiyar Lahadi yayin musayar wuta da jami’an ‘yan sanda na babban birnin tarayya, biyo bayan amsa wani kiran gaggawa.

Kamfanin dillacin labarai na PRNigeria ta ruwaito cewa ‘yan bindigan sun afka wa kauyen Naharati ne da ke karamar hukumar Abaji, kuma suna shirin sace wasu mazauna garin, kafin ‘yan sanda su ka dakile harin nasu.

Majiyar ‘yan sanda ta ce masu garkuwar biyu sun mutu ne daga rauni bayan an kai su asibiti, yayin da rundunar ta fara farautar sauran maharan da suka tsere.

Rahoton ya kara da cewa Jami’an ‘Yan Sandan sun cafke mutum 5 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne a shiyar unguwar Lugbe, yayin sintirin da suka saba yi a ranar Juma’a.

Wadanda ake zargin sun furta cewa su mambobin kungiyar ‘Aro Baga ne, wadanda suka addabi yankin unguwar Gwagwa. Bindigogin da aka kwato daga hannunsu sun hada da karamar bindiga kirar gida da harsasai.

ASP Yusuf Mariam, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta FCT, a cikin wata sanarwa, ta kara bayyana cewa jami’an‘ ‘yan sandan sun kuma kama wata mai suna Blessing Nuhu, mai shekaru 24; da kuma Ifeoma Nnamuchi, shekaru 31, jagororin ‘yan fashi dake aika-aika a shiyar Lugbe zuwa Galadinmawa. Za’ a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, Inji ASP Yusuf Mariam

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button