Labarai

Jami’an tsaro na cikin shirin ko ta kwana a Kaduna sakamakon tashin hankalin da zai biyo bayan zabe – Gwamnatin Jiha

Spread the love

Gwamnatin jihar Kaduna ta bukaci mazauna jihar da su guji tashin hankali saboda duk hukumomin tsaro a jihar suna cikin “tsattsauran shiri” don dakile barazanar doka da oda.

An sanar da sakamakon kananan hukumomi 19 daga cikin 23 na jihar a ranar Lahadi kafin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta dage tattara sakamakon zaben.

Bayan ci gaba da aiki, ana sa ran za a sanar da sauran 4 a ranar Litinin da yamma.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro na cikin gida Samuel Aruwan ya fitar a ranar Litinin, gwamnatin jihar ta samu bayanan sirri da ke nuni da shirin wasu mutane da kungiyoyi na haddasa rikici a cikin babban birnin Kaduna da wasu manyan cibiyoyi a jihar.

“Hukumomin tsaro na gudanar da bincike mai zurfi kan wadannan rahotanni. Mutane da kungiyoyin da aka samu suna da hannu a irin wadannan ayyuka za a gurfanar da su a gaban kuliya,” inji Aruwan.

“Yana da mahimmanci a sake nanata cewa an haramta zanga-zangar kan tituna don hana duk wani abu da zai iya haifar da rugujewar doka da oda.

“Gwamnati ta yi kira ga ‘yan kasa da su bayar da bayanai kan duk wani aiki da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya, doka da oda ta wannan layukan taimako: 09034000060 08170189999.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button