Labarai
Jami’an ‘yan Sanda sunyi Awon Gaba da me Jaridar Sahara Reporters ~Sowore
Rahotanni daga Abuja sun Tabbatar da Cewa Jami’an tsaron Najeriya sun kame mawallafin Jaridar Sahara Reporters wato Omoyele Sowore, da sauran wasu masu fafutuka a Abuja wadanda ke gudanar da jerin gwanon nuna murnar shiga sabuwar shekara a Abuja.
Shaidun gani da ido sun ce ‘yan sanda da ake zargi suna tare da’ Rapid Response Squad ‘sun mamaye mahadar Gudu a Abuja, inda ake Zargin sunyiwa Sowore rauni kafin su dauke shi tare da wasu masu fafutuka a wurin.