Ilimi
Jami’ar Bayero Ta Kano Ta Yi Rashin Shehin Malami.

Allah ya yiwa Mataimakin Shuagaban Gudanarwa na Jami’ar Bayero Kano Farfesa Haruna Wakili rasuwa.
Ya rasu yana da shekara 60 a safiyar Asabar da asuba a babban asibitin kasa da ke Abuja bayan wata doguwar jinya.
Jaridar Dailytrust ta rawaito cewa za a binne marigayin malamin a garinsu da ke Hadejia, Jihar Jigawa.
Wakili shi ne tsohon Daraktan Bincike da Koyarwa (Gidan Mambayya).
Hakanan ya kasance Kwamishinan Ilimi a Jihar Jigawa.