Jami’ar Kaduna ta kori Malami saboda ya rungune Ɗaliba Mace a Ofishinsa.
Jami’ar jihar Kaduna, KASU, ta dakatar da Dakta Idowu Abbas na sashen nazarin kasa, kan zargin cin zarafin mata.
Mataimakin Shugaban Kwalejin (Ilimi) na makarantar, Farfesa Abdullahi Ashafa, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a Kaduna a ranar Juma’a, 15 ga watan Janairu Ashafa ya kuma sanar da karin girma ga wasu malamai 12 na makarantar.
A cewar Ashafa, Babban Kwamitin Ladabtar da Ma’aikata na jami’ar, wanda Mataimakin Mataimakin Shugaban Jami’a (Gudanarwa) ya jagoranta, ya binciki zargin cin zarafin da aka yi wa malamin. An gabatar da rahoton kwamitin binciken ne a taron gudanarwa na 217 na makarantar a ranar 12 ga Janairu.
Ya ce, shugabannin sun kori Abbas daga aikin jami’a tare da bayar da umarnin a mayar da duk daliban da ke karkashin kulawar sa zuwa wani malami mai nagarta a sashen.
“A cewar rahoton, Abbas ya furta a cikin shaidarsa cewa ya taba tare da rungumar wata daliba mace da yake lura da aikinta ta baya ba da son ranta ba lokacin da ta je ofishinsa don tattauna aikin nata.
Shaidun nasa sun kuma bayyana wasu munanan halayen rashin kirki da ya nuna wa ɗalibin.
Wannan mummunan halin ya saba wa Sashe na 8.7 sakin layi (f) na Dokokin Gudanarwa da Tsarin Ilimi a Jami’ar Jihar Kaduna.
Dokokin sun ce ‘cin zarafi / musgunawa da dalibai ta hanyar jarrabawar ce ta kora daga aiki da kuma dakatar da nadin,’ ‘in ji shi.
Mataimakin Shugaban ya bayyana murabus din da Abbas yayi a baya a matsayin “banza da wofi.”