Jami’in Dan Sanda ya harbe direban keke naped kan cin Hancin naira dari N100
Rundunar ‘yan sanda a jihar Ribas, Kudu maso Kudancin Najeriya, ta tabbatar da cewa wani jami’insu ya harbe wani matukin babur mai kafa uku (keke) a Fatakwal da safiyar Alhamis.
Matasa da masu tuka keken, wadanda Lamarin ya fusata sun ta kutsawa cikin yankin da aka yi harbin.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Nnami Omoni, ya ce an kama jami’in, “wanda ya kawo kansa gare su, an tsare shi.
Mista Omoni ya ce Dan Sandan zai fuskanci shari’a nan take don ya zama abin koyi ga wasu masu Sha’awar aikata Haka ,” in ji Mista Omoni wanda ya kara da cewa har yanzu bai samu cikakken bayanin abin da ya faru ba.
Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa an kashe wanda aka kashe din ne saboda ya ki baiwa jami’in cin hancin N100.
Jaridar ta wallafa faifan bidiyon wanda aka kashe din kwance cikin jini, tare da mutane biyu sun durkusa suna kuka a kan gawar.
Mai magana da yawun ‘yan sandan, Mista Omoni, ya ce‘ yan sanda na kokarin shawo kan mummunar fadan da ya barke sakamakon lamarin.