Fashion
Jamila Nagudu Ta Yi Murnar Zagayowar Haiwuwarta.

Jamila Nagudu Ta Yi Murnar Zagayowar Haiwuwarta.

A yau dinnan jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa Kannywood Jamila Umar Nagudu tayi murnar zagayowar ranar haiwuwarta.
Tuni masoya da ‘yan uwa da abokan sana’arta suka aike mata da sakon taya murna da kuma fatan alkhairi agareta.
A nata bangaren, jarumar cikin farin ciki da annushuwa take godiya ga daukacin wadanda suka tayata murna.
Jamila Nagudu Ta kara da cewa tana alfahari da masoyanta, wadanda a koda yaushe suke yimata fatan alkhairi da fatan samin daukaka a rayuwarta.
Sai dai kuma tambayar da jama’a sukafi so suji amsarta daga bakin jarumar itace, shekarunta nawa?