Jam’iyar APC Mai Mulki Tayi babban Kamu a Jihar Adamawa…
Wani jigon siyasa kuma tsohon Dan takaran sanata a jamiyyar SDP a jihar Adamawa, Alhaji Abdurrahman Buba Kwaccham ya fice daga jamiyyar, tare da sauya sheqa zuwa jamiyyar APC mai mulki. Alhaji Abdurrahman Kwaccham ya koma jamiyyar ta APC ne bayan buqatar hakan daga wasu jagorin jam’iyyar a jiharsa ta Adamawa, kamar yadda ya yiwa jaridar….bayani a yau Lahadi a Birnin Abuja.
Kwaccham wanda har ila yau shi ne shugaban qungiyar matasa a jihohin Arewa maso Gabar mai suna (Movement of North East Youths Organisation Forum) a turance, ya ce jagorin jam’iyyar ta APC na matsayin iyaye ne a gare shi kuma ba zai iya tsallakewa buqatarsu ba.
…..ta samu labarin cewa, jigogi a jam’iyyar APC daga jihar ta Adamawa da su ka shawo kan Kwaccham wajen komar jam’iyyar ta su, sun haxa da Janaral Muhammad Buba Marwa mai ritaya, wanda ke matsayin shugaban kwamitin shugaban qasa kan kawar da miyagun qwayoyi a Najeriya. Da malam Nuhu Ribadu tsohon shugaban Hukumar EFCC, kuma jigo a jam’iyyar APC a jihar Adamawa.
Da Farfesa Tahir Mamman, sakataren kwamitin riqo na jam’iyyar APC shiyyar jihohin Arewa maso Gabar (Qarqashin gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni da ke matsayin shugaban kwamitin a mataki na qasa). Sauran jagororin jam’iyyar da su ka yi zawarcinsa sun hada da Sanata Bello Tukur, tsohon mataimakin Gwamna a jihar Adamawa kuma wanda ya taba wakiltar yankin Adamawa ta tsakiya a majalisar dattawa, da dai sauransu. Jagororin jam’iyyar ta APC daga jihar Adamawa sun haxu wajen miqawa matashin Xan siyasan, tutar jam’iyyar a yayin wata ganawa a birnin Abuja a ranar Lajadin nan, kamar yadda Kwaccham xin ya sanar da…….
Da ya ke qarin haske a kan lamarin, Alhaji Abdurrahman Buba Kwaccham, wanda ya ce “Lamarin ya zo mini a matsayin bazata, amma wanda na tabbata alheri ne. Ya qara da cewa jam’iyyar siyasa tamkar tsani ce, da za a iya amfani da ita wajen kai cigaba ga al’umma, inda ya yi fatan hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan cigaba ga jiharsa ta Adamawa da ma yankin arewa maso gabar baki xaya, kamar yadda ya yi bayani.
Haka nan ya ce zai yi dukkan mai yiwuwa wajen samar da cibiyar kasuwanci mara harajin sauqe kayan masana’antu a Garin Mubi wato (Free Trade Zone) don habaka harkan masana’antu da kasuwanci da zai samar da ayyukan yi a yankin da ke iyaka da qasar Kamaru. Haka nan ya ce zai kuma yi qoqari wajen tabbatar da kafa cibiyoyin koyar da sana’oi a yankin da kuma qarisa aikin babban asibitin Garin Mubi, zuwa matakin na koyarwa ga jami’ar jihar Adamawa.