Siyasa

Jam’iyyar APC ta taya Gwamnan Edo, Obaseki murnar Yin Nasara.

Spread the love

Jam’iyyar APC ta taya Gwamna Godwin Obaseki murnar sake zaban shi na gwamnan jihar Edo.

Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC na kasa, Mai Mala Buni ya fada a cikin wata sanarwa cewa gudanar da zaben cikin lumana da kuma sakamakonsa na nuna nasara ga dimokuradiyyar Najeriya.

Ya ce jam’iyyar da shugaban kasa na nan kan bakan su na ganin an gudanar da sahihin zabe na gaskiya don karfafa tushen ikon siyasa da dabi’ar kasar.

Ya yaba wa INEC, hukumomin tsaro, da dukkan jam’iyyun siyasar da suka fafata a zaben bisa nasarar gudanar da zaben cikin lumana.

Ya kuma yaba wa fitaccen dan takarar jam’iyyar Fasto Osagie Ize-Iyamu saboda jajircewarsa da shugabancinsa yayin da ya yaba da kokarin Tsohon shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole, da sauran mambobin don nuna goyon baya ga jam’iyyar da dan takararta a zaben.

Gwamna Buni ya kara da cewa lokaci ya yi da za a hada kai don ciyar da dimokuradiyyar kasar gaba tare da kawo karshen zamanin da yakin neman zabe ya zama tamkar yaki.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button