Jam’iyyar PDP Ta Shirya Karbar Gwamnan Jahar Edo Mr Obaseki.
Bayan hanashi tikitin tsayawa takarar Gwamnan Jahar Edo a karo ma biyu, Gwamnan Obaseki ya shirya komawa jam’iyyar PDP mai adawa.
Duk da cewa yanzu haka Gwamna Obaseki yana birnin tarayyar Nijeriya Abuja, amma Ana tsammanin komawarsa babban birnin jaharsa ta Edo Wato Benin a yau dinnan.
Chiyaman jam’iyyar PDP Na Jahar Edo Tony Azegbemi shine tabbatarda wannan labari wa mane ma labarai.
Tony ya bayyana cewa yanzu haka sun shiryawa Katin shigowar Mr Obeseki ta kammala.
Sai dai zaben Gwamna a jam’iyyar ta PDP zai kasance a ranar juma’a dakuma assabar Wato 20 ga watan June zuwa 23 June 2020.
Idan dai ba’a manta Gwamnan Obaseki ya rasa tikitin tsayawa takarar Gwamnan Jahar Edo bayan ziyartar shugaba Buhari a fadarsa dake Aso Rock Villa.
Daga Abdullahi Muhammad Maiyama