Siyasa

Jam’iyyar SDP Ita Ce Jam’iyya Ta Uku Wadda Ta Taka Rawar Gani Acikin Jam’iyyu 18 Da Sukayi Takarar A Zaben Da Ya Gabata~Dr. Abdul Ahmad Ishaq.

Spread the love

Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), na daga cikin jam’iyyu 18 wadanda muke dasu a Najeriya.

Jam’iyyar SDP dai jam’iyya ce wadda ta taka rawar gani a zabuka daban-daban da suka gabata.

Dr. Abdul Ahmad Ishaq shine Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, mun sami zantawa dashi a garin Kano, yayin wata ziyara da yakai ofishin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano a Karkashin inuwar jam’iyyar SDP a zabe shekarar 2019 da ya gabata, wato Alh. Bello Ado Hussaini.

Da farko dai Dr. Abdul ya yi mana takaitaccen bayani akan irin rawar da jam’iyyarsu take talawa ta fuskar cigaban dimokuradiyyar Najeriya, inda yace “Wannan Jam’iyya tamu ta Social Democratic Party ba sabuwar Jam’iyya bace, domin kuwa a shekarar 1992 Zuwa 1993 anyi takarar tsakanin Jam’iyyarmu ta SDP da kuma jam’iyyar NRC a zabuka maban-banta a kasarnan.”

Da muna da Jam’iyyu guda 91 Zuwa 92 a Najeriya, amma a yanzu kuwa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kori wajen guda 74, yanzu sauran jam’iyyu guda 18 suka rage a Najeriya.

“Acikin jam’iyyu 18 din da muke dasu a Najeriya, Wadanda suka fito da ‘yan takar-karu, kuma suka taka rawar gani, jam’iyyarmu ta Social Democratic Party ita ce ta Uku a Najeriya.”

Dr. Abdul Ahmad Ishaq ya kara da cewa “Manufar jam’iyyarmu ita ce kawo mutanen da suka can-canta, wadanda suke da ilimi da wayewa, masu Fasaha kuma jajirtattu wadanda za su inganta rayuwar Talaka ta hanyar bashi ingantaccen Ilimi, Ingantacciyar Lafiya, bunkasa harkar Noma, sufuri da sauransu. Da wadannan abubuwan ne Talakawa suke aunawa suga shuwagabanninsu suna da adalci ko akasin haka.”

Dr. Abdul Ahmad Ishaq ya nuna gamsuwarsa game da yadda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari take yaki da rashawa, inda yace “Alƙawarin da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yiwa ‘yan kasa shine yaki da cin hanci da rashawa, saboda shine abin da yayiwa jama’a katutu a wancen lokacin, saboda wadanda suke cin hanci da rashawa a wancan lokacin sune mutanen da al’umma suke so, sune abin yabo agaresu. Tabbas gwamnati tana yaki da cin hanci da rashawa.”

Daga karshe Dr. Abdul ya shawarci shugaba Buhari da ya zakulo mataimaka da jagororin yaki da cin hanci rashawa nagrtattu kuma jajirtattu, wadanda za su fitar dashi daga jin kunyar ‘yan Najeriya, inda yace “Abin da ya kamata shugaban kasa yayi shine yasami mataimaka da shuwagabannin Hukumomin Yaki Da Cin Hanci ƙwararru Tsayayyu nagartattu jajirtattu wadanda za su binciki duk wanda yayi ba dai dai ba.”

Ya kara da cewa “Shi Shugaban kasa Muhmammadu Buhari duk wani tarihinsa da labarinsa idan ka bincika za ka ga shi mai gaskiya ne da rikon amana, kuma ba shugaban kasa Muhmammadu Buhari ne kadai ne yake mulki a Najeriya ba, akwai mataimaka da wakilai da masu mukamai daban-daban har zuwa Kansila. Ba shugaban kasa ne zai je yankinku ya binkici matsalarku ba, akwai wakilai tun daga kan Kansiloli har zuwa sama, wadanda suka fito daga yankunanku. Idan kuna da matsala kamata yayi kufara nemansu kafin kunemi shugaban kasa.” Inji Dr. Abdul Ahmad Ishaq, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button