Siyasa
Jam’iyyar SDP Ta Zargi APC Da Kai Mata Hari Da Bindugu A Ondo.
Jam’iyyar SDP ta Zargi Jam’iyya mai mulki ta APC Da kai hari kan Tawagar ta lokacin da Suke Gudanar da Yakin Neman Zabe a Garin Idanre Na Jihar Ondo.
A wata sanarwa da Dantakarar Jam’iyyar a Idanre Bankole Akinselure ya Fitar Jiya Talata, yace Membobin Jam’iyyar APC Sun Fara Kai Musu Harin ne Duba da Yadda Suke Ganin SDP zata musu mummunar Kaye a Zaben da za’a gudanar Ranar Asabar mai zuwa.
Akinselure ya yi Ikirarin An kai musu harin da Manyan bindigu Inda yace ya
yan Jam’iyyarsu sun Tsira da Raunuka yayin Harin, Sannan Maharan sun lalata Motoci da Mashina Na Mambobinsu Inji Shi.
Akinselure yace wannan Halamun Nasara ce Ga Jam’iyyarsu a Zaben da za’a Gudanar Ranar Asabar mai Zuwa.
Ahmed T. Adam Bagas