Labarai

Jarabawar WAEC: Sanata Uba Sani Ya dauki nauyin ‘ya ‘yan talakawa har mutun dari da Hamisin 150.

Spread the love

A cigaba da Taimakon Al’ummar da Sanata Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya ya keyi Sanata Malam Uba Sani har’ila yau ya dauki nauyin kudin Zana Jarabawar WAEC din Yara maza da mata ‘ya ‘yan talakawa ‘yan Asalin Jihar kaduna Har sama da mutun dari da hamisin 150+  a duk kokarinsa na ganin Matasan sun samu ingantaccen Ilimin sanin darajar rayuwa.
Sanatan Kuma ya dauki mutun ashirin  da biyar 25 dake mazabu da ban da ban  wa’yanda yanzu Haka su ke aiki a karkashin sa duk domin sanin halinda Al’ummar da yake wakiltar Suke Ciki na halin lafiya ko akasin Hakan…


Sanatan dai Yace babban burinsa yanzu shine kawo karshen matsalar jahilci da zaman Banza a Cikin Al’ummar da yake wakilta da kaduna izuwa Arewacin Nageriya Baki daya…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button