Jargin Fasinja Na Farko Daga Kasashen Waje Ya Sauka A Birnin Lagos A Jiya Asabar.
Jargin Fasinja Na Farko Daga Kasashen Waje Ya Sauka A Birnin Lagos A Jiya Asabar
A Karon farko tun bayan watanni 5, jirgin saman fasinja daga kasashen waje ya sauka a birnin Lagos na kudancin tarayyar Najeriya a jiya Asabar.
Kamfanin dillancin labaran NAN na gwamnatin tarayyar Najeriya ya bayyana cewa jirgin kamfanin “Midle East Airline” daga birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon ya sauka a tashar jiragen sama ta Mutala Muhammad International Airport da ke birnin Lagos da misalign karfe 2.30 na rana dauke da fasinja kimani 200.
Tun cikin watan Maris na wannan shekarar ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta rufe tashoshin jiragen saman kasar gaba daya, saboda hana yaduwar cutar Korona.
Labarin ya kara da cewa jami’an hukumomin daban –daban wadanda suka hada da Custom, shige da fice da sauransu duk sun shirya kafin isar Jirgin.
Labarin y ace ma’aikatan sun yi farin ciki da zuwan jirgin na farko. Don fatan cewa rayuwa za ta koma kamar da a tashar jiragen saman.
Labarin ya kammala da cewa fasinjojin jirgin sun hada da yan kasa da kuma wasu daga kasashen waje. Kuma tuni sun fara bin sabon tsarin kiwon lafiyan wanda aka shimfida na shiga kasar. (19)
Daga Haidar H Hasheem Kano