Ga wasu Lai fuka Goma 10 da ake zargin magu dasu…
1- tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato daga hannun barayin gwamnati.
2-ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn.
3-rashin biyayya ga ofishin Antoni janar Na kasa.
4-bata lokaci wajen binciken kamfanin B&ID Wanda hakan ya haifar da rikicin da akeyi a kotu yanzu
5-rashin isassun hujjoji domin dawo da diezani Alison madueke Nigeria.
6-kin bin umarnin kotu wajen sakin asasusn wani tsohon daraktan
banki kimanin N7bn.
7-bata lokaci wajen daukar mataki kan wasu jiragen ruwa biyu da hukumar sojan ruwa ta kwace.
8-fifita wasu Jami an EFCC fiye da wasu wadanda ake kira da MAGU boys.
9-kai wasu alkalai kara wajen shugabannin su batare da sanin Antoni janar ba.
10-sayar da dukiyoyin sata ga yan uwansa da abokan arziki.
Daga Kabiru Ado Muhd