Jiga Jigan Jam’iyyar APC Na UK Da Sauran Kasashen Waje Sun Yabawa Shugaba Buhari Da Hafsoshin Tsaro Saboda Kokarin Da Suke A Yaki Da Hoko Haram.
Jiga-jigan Jam’iyyar APC na UK da dukkanin kasashen waje sun yabawa Shugaba Muhammadu Buhari da Shugabannin tsaro saboda nuna kishin kasa da kwazo a yakin da ake yi da ta’addanci.
Saboda himmatuwarsu ga kawo karshen ta’adancin, kungiyoyin APC a cikin kasashen waje sun yi alƙawarin tattara tallafi da bada don cikakken goyon baya ga ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya a aikin share fage na ƙarshe.
Bayan yin zurfin nazari kan abin da ya faru a yankin Arewa Maso Gabas, kungiyoyin APC sun ba da tabbacin cewa an samu cigaba sosai ta hanyar sojojin tun lokacin da aka sauya shugaban Hafsin Sojan Laftanar Janar TY Buratai.
A wata sanarwa dauke da sa hannun Dokta Philip Idaewor, Shugaban Jam’iyyar APC na UK da kuma Shugaban Kwamitin Shugabannin ‘yan kasashen waje, kungiyoyin sun bayyana yadda aka kashe manyan kwamandojin Boko Haram / ISWAP, wasu da dama kuma suka jikkata, suna gudu zuwa kasashen da ke makwabta.
“Mun lura cewa Sojojin Najeriya sun samu nasarori a kan ‘yan ta’addar Boko Haram sakamakon komawar Babban Hafsan Sojojin, Laftanar Janar TY Buratai zuwa fagen daga, wanda hakan ya sa aka dauki yakin zuwa sansanin’ yan ta’addan.
Wannan kisan-kiyashi ya sa aka lalata sansanonin ‘yan ta’adda tare da kashe manyan kwamandoji na kungiyar masu, yayin da sauran ‘yan ta’adda suka tsere zuwa kasashe makwabta kamar yadda suke yi koyaushe, ”in ji Dr Idaewor.
“Mun kuma lura cewa ‘yan Boko Haram sun yi garkuwa da ma’aikatan agaji tare da kashe su.”