Labarai
Jihar Kaduna ce ke kan gaba a Arewacin Najeriya wajen Tara ku’din Haraji ya yin da Gwamnatin Uba sani ya Samar da naira biliyan 62.49bn.
Shugaban Hukumar Harajin Harajin Cikin Gida ta Jihar Kaduna, Jerry Adams, ya bayyana cewa Kaduna ta samu Naira biliyan 62.49 a cikin kudaden shiga na cikin gida a shekarar 2023 ita ce mafi girma a Arewacin Najeriya.
A cewarsa, manufofin Gwamna Uba Sani kan hada-hadar kudi, fadada tushen haraji, da sake tsara ayyukan shigar da kudaden shiga na jihar ne suka haifar da karuwar kudaden shiga na cikin gida a jihar Kaduna.
Adams ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar, inda ya bayyana cewa matsayin Kaduna a matsayin ta na jiha da ke da mafi yawan kudaden shiga a arewa a shekarar 2023, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa ta ruwaito, ya samu karbuwa sosai.