Rahotanni

Jihar Kaduna tayi Rashin Uba Inji El Rufa’i, za’ayi Jana’izar sa da misalin karfe 05:00pm

Spread the love

Gwamnan jihar kaduna Malam Nasiru El Rufa’i ya ce a yau ina cike da bakin ciki ina Mai tabbatar da rasuwar mahaifin jiharmu, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alh (Dr.) Shehu Idris CFR. Ya rasu ne a Asibitin Sojoji na Kaduna da ke Kaduna a yau bayan gajeriyar rashin lafiya. An shirya sallar Jana’izarsa  a Zariya da misalin karfe 5 na yamma in Sha Allah. Za’abi tsarin kiyayewa na Covid-19 a lokacin addu’ar Jana’izarsa 

El Rufa’i Yace Na sanar da Shugaba Muhammdu Buhari, GCFR babban rashin kuma na yi mana ta’aziyya. Shugaban Ma’aikata na PMB, Farfesa Ibrahim Gambari zai jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Zariya don ta’aziyya ga dangin Mai martaba, Shugaban Majalisar Masarautar Zazzau da mutanen Masarautar Zazzau da Jihar Kaduna. Munyi rashin abin alfahari, tushen hikima da shiriya kuma uba na kwarai ga kowa. Da fatan Allah Ya ba da ransa mazauni a Aljanna Firdaus. Amin. – Nasir El-Rufai

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button