Ilimi
Jihar Legas Ta Ba Da Sanarwar Sake Bude Makarantun Gwamnati.
Za a sake nazarin tsari mai gudana da kuma bin shawarwarin Ma’aikatar Lafiya.
Gwamnatin jihar Legas ta umurci dukkanin makarantun da ke mallakar jihar su koma ranar 14 ga Satumbar.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana hakan ranar Asabar.
Sanwo-Olu ya ce “ba a yanke wannan hukunci a kan dutse ba kuma za a duba batun tsari mai gudana da kuma shawarar ta fito daga Ma’aikatar Lafiya,” in ji Sanwo-Olu.