Jihohi Kano, Borno, Katsina da kuma Legas a halin yanzu sun kasance a matsayi mafi girma a matakin karancin abinci – UNICEF
.
Asusun kula da ilmin yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce sakamakon bincikensu ya nuna cewa gwamnatocin tarayya da na jihohi ba sa kashe isassun kudade da za su magance matsalar karancin abinci mai gina jiki a Najeriya.
Ya ce jihohi hudu – Kano, Borno, Katsina da kuma Legas – a halin yanzu sun kasance a matsayi mafi girma a matakin karancin abinci.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana bukatar makudan kudade don taimakawa wajen gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a a yankunan da ke nesa da kuma samar da tallafi ga yaran da ke fuskantar matsanancin rashin abinci mai gina jiki a kasar.
Da yake magana a ranar Laraba, a wajen bude taron yini biyu kan tattaunawa kan harkokin yada labarai da samar da abinci mai gina jiki a Najeriya, wanda aka gudanar a garin Fatakwal na jihar Ribas, kwararre kan harkokin sadarwa na UNICEF, Mista Geoffrey Njoku, ya ce tattaunawar an yi ta ne domin gano gibin kudaden da ake samu a kasa da kasafi don magance matsalolin rashin abinci mai gina jiki da yadda za a cike gibin.
Jami’in kula da abinci mai gina jiki na UNICEF Nkeiru Enwelum, wanda ya gabatar da kasida mai taken, “Halin abinci mai gina jiki a Najeriya, ya bayyani na rashin abinci mai gina jiki a Najeriya da kuma illar da ke tattare da kananan yara,” ya ce a halin yanzu kimanin yara miliyan 35 a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki.
“Kimanin yara miliyan 35 daga cikin yara ‘yan kasa da shekara biyar a Najeriya, kuma a cikin wannan muna da miliyan 12 daga cikinsu na fama da tamowa. Kuma muna da kusan miliyan uku da rayukan su suka salwanta a Najeriya,” inji ta.
Dangane da kididdigar da aka yi, Enwelum ya ce Najeriya ce ta daya a Nahiyar Afirka a kan bayanai kan yara da ke fama da tamowa kuma ta biyu a duniya.
Dangane da bayanan yunwa da karancin abinci, ya ce mutane miliyan 17.7 na fama da yunwa a Najeriya.
Enwelum ya kuma ce kimanin mutane miliyan daya ne ke fama da matsanancin karancin abinci a Najeriya.
A cewarsa jihohin da suka fi fama da matsalar karancin abinci a Najeriya sun hada da Kano da Legas.
Duk da cewa jihohin Kano da Borno da Katsina da kuma Legas ne ke kan gaba a matakin karancin abinci, ya ce matsalar karancin abinci mai gina jiki ta yadu a kasar, lamarin da ke shafar mutanen da ke zaune a wasu sassan kasar.
Ya kara da cewa wasu cututtuka ko sakamakon rashin aikin jiki ne ke kawo su, daga rashin abinci mai gina jiki aka san su, anemia, rickett, rashi bitamin A (xerophamia).
Enwelum, ya kuma bayar da kima kan ci gaban da ake samu kan harkokin kiwon lafiya, yana mai cewa shayar da jarirai nonon uwa zalla ita ce kawai bangare na SDG da Najeriya ke samun ci gaba kuma mai yiwuwa ta cimma burin nan da shekarar 2030.