Jikana ya rasu ne sakamakon rashin kulawa da lafiyar sa a Asibitin Gwamnati -Akpabio
“Ba likita, ba ma’aikacin jinya. Ya zubar da jini har sai da ya rasa kashi 60 cikin 100 na jininsa kuma ya kusa fita hayyacinsa, ya yi ta fama ya fadi kasa.”
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana yadda ya rasa jika sakamakon rashin lafiya da ya yi a wani asibitin gwamnati.
Ya fadi haka ne a ranar Juma’a a yayin da ake tantance ministoci a benen majalisar dattawa a Abuja.
Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ya yi magana ne a lokacin da ake tantance Tunji Alausa a matsayin wanda Bola Tinubu ya zaba a matsayin minista.
Yayin da Alausa yake bayani tare da samar da mafita ga al’amurran da suka shafi tsarin kiwon lafiyar Najeriya, dan majalisar ya amince da kasancewar bangaren a matsayin wanda aka yi watsi da shi.
Akpabio ya ce “Kowane mutum yana fama da rashin kulawar likita.”
“Jikana na farko a shekarar 2019 a cibiyar kula da lafiya ta tarayya ya mutu sakamakon zubar jini. Yana karbar drip kuma an goge shi a cikin dare – babu wani taimako,” in ji tsohon gwamnan.
“Ya kasance yana neman ruwan sha. Ya yi birgima a waje ya shiga raɓa. Babu likita, babu nas. Ya zubar da jini har sai da ya rasa kashi 60 na jininsa kuma ya kusa fita hayyacinsa, yana fama ya fadi kasa.
“A lokacin, ya shiga suma,” in ji Sanata Akpabio.
Ya ci gaba da ba da labarin abin da ya faru, ya ce: “Na yi kokawa. Sun je suka kawo na’ura don kokarin farfado da zuciya, amma hakan bai yi tasiri ba”.
“Na yi amfani da hannuna kuma na yi fama da likitana, na kasa farfado da shi. Sai na rufe idonsa na ajiye shi a dakin ajiyar gawa,” in ji Akpabio.