Labarai

Jima’i da mace kamar sau Ashirin da daya 21 a cikin wata guda na hana Mazaje kamuwa da manyan cuta ~Binciken likita.

Spread the love

Kamar yadda premium time suka ruwaito sun ce Wani likita mai suna Dr Ken ya yi kira ga maza da su rika yin jima’i akalla sau 21 a wata domin samun kariya daga kamuwa da cutar dajin dake kama ‘ya’yan mairainai.

Ken ya fadi haka ne da yake hira da shirin kafar radiyo na ‘Classic FM, 97.3.’

A Shirin dake ta taken ‘A tattauna’ Ken ya shawarci mazaje da su kara yawan lukuttan saduwa da iyali domin kaucewa kamuwa da irin wannan cututtuka.

Cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraina cuta ce dakan hana namiji yin fitsari da kuma wasu illoli masu yawa. Idan ba a maida hankali a kai ba sai ka ga har an rasa rai.

Cutar ya fi kama maza masu shekaru 40 zuwa sama.

Binciken Dubawa da Abin da likitoci suka ce.

Dubawa ta gudanar da binciken domin gano ko akwai gaskiya a bayanan da Ken ya yi.

Sakamakon binciken da gidauniyar ‘Urology Care’ ta gudanar a 2004 kan amfanin yawan fitar da maniyi ga namiji ya nuna cewa mazan dake yawan fitar da maniyi a jikinsu na samun kariyar kashi 20% na gujewa kamuwa da dajin dake kama ya’yan marainan.

Duk da haka gidauniyar ta ce za ta zurfafa gudanar da bincike a kai domin samun Karin haske.

Wani sakamakon binciken da aka gudanar a 2016 ya nuna cewa yawan fitar da maniyi ga namijin da ya dara shekaru 50 na kare shi daga kamuwa da cutar da maza matasa masu shekaru 20 zuwa 40.

Duk da hakan Dubawa ta ce wannan batu ne da ya kamata a zurfafa gudanar da bincike a kai domin samun Karin haske.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button