Jiragen ruwa 33 dauke da kayan more rayuwar Talaka suna kan hanyar zuwa Nageriya
Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA, karkashin Jagorancin hadiza bala usman a ranar Juma’a ta ce tana tsammanin jiragen ruwa guda 33 dauke da kayayyaki da mai, kayayyakin abinci da sauran kayayyaki daga 3 ga Yuli zuwa 16 ga Yuli. Hukumar NPA ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar ta, ‘Wannan sanarwa wacce kwafinta takardar ya isa ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya ne a Legas ranar Juma’a. A cewarta, ana sa ran jiragen za su isa Filin Jirgin Saman TinCan Island. Rahoton ya ce jiragen sun ƙunshi kwantena, jigilar kayayyaki, alkama mai yawa, tare da motocin da ake Anfani dasu da gishiri mai yawa, tare da man fetur.
Rahoton NPA ya ce jiragen ruwa 16 sun isa tashar jiragen ruwa, suna jira don jigilar kayayyakin kungiyar ta ce wasu jiragen ruwa shida sun kasance a tashar jiragen ruwa wadanda ke sauke kwantena, yanzu haka…