Labarai
Jirgin Ruwa Mafi Girma Ya Zo Gabar Ruwan Najeriya.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Jirgin ruwa mafi girma da ya taba zuwa Najeriya ya isa gabar ruwa ta Onne Port a garin Fatakwal jihar Rivers.
Jorgin tuwan me suna Maerskline Stardelhorn ya fitone daga kasar Singapore inda ya iso gabar ruwa ta Najeriya a jiya, Asabar. Mun samo muku cewa jirgin ruwan na da tsawon mita 300 da kuma fadin mita 48.
An aika jirgin ruwan zuwa Fatakwal ne dan a ragewa tashar jirgin ruwa ta Legas cunkoso.